Dan China ya makale a cikin injin wanki
An ceto wani dan China da yake zaune a lardin Fujian da ke kasar, wanda kansa ya makale a cikin injin wanki yayin da yake kokarin gyarawa bayan da ya lalace a ranar Lahadin da ta gabata.Wadansu ’yan kwana-kwana ne da ke yankin suka yi nasarar fitar da shi daga cikin injin bayan ya kwashe […]
An ceto wani dan China da yake zaune a lardin Fujian da ke kasar, wanda kansa ya makale a cikin injin wanki yayin da yake kokarin gyarawa bayan da ya lalace a ranar Lahadin da ta gabata.
Wadansu ’yan kwana-kwana ne da ke yankin suka yi nasarar fitar da shi daga cikin injin bayan ya kwashe lokaci mai tsawo yana yunkurin yin hakan ba tare da samun nasara ba.
Da farko dai sai da ’yan kwana-kwanan suka fara fitar da kan mutumin ne daga wani bangare na injin don su tabbatar da cewa ya ci gaba da samun isasshiyar isakar lumfashi. Kafin daga bisani su fara fasa robar da kansa ta makale a ciki, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta bayyana.
Bayan an ceto mutumin daga injin, an garzaya da shi asibiti inda likitoci suka duba shi kuma suka tabbar da cewa yana cikin koshin lafiya. Sai dai ba a bayyana sunan mutumin ba.
Kafar yada labaran CNN ta ce ba wannan ne karo na farko da jami’an kwana-kwanan kasar China suka ceto mutanen da suka shiga mawuyacin hali ba.
Ko a watan Afrilun da ya gabata ma, ’yan kwana-kwana kasar sun ceto wani yaro da kansa ya makale a tagar da ke saman mota.