Dan fashi ya zargi mahaifinsa kan rashin ba shi tarbiyya
Wani mutum mai suna Adeyemi Morenikeji mai shekara 37, ya fashe da kuka lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani inda ya ce shi ne ya kashe matar tsohon mai gidansa ta hanyar makure ta kafin ya yi awon gaba da motarta, inda ya zargi mahaifinsa da rashin ba shi tarbiyya. Adeyemi ya bayyana […]
Wani mutum mai suna Adeyemi Morenikeji mai shekara 37, ya fashe da kuka lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani inda ya ce shi ne ya kashe matar tsohon mai gidansa ta hanyar makure ta kafin ya yi awon gaba da motarta, inda ya zargi mahaifinsa da rashin ba shi tarbiyya.
Adeyemi ya bayyana haka ne lokacin da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo Mista Shina Olukolu ke nuna shi ga ’yan jarida. Kwamishinan ya ce Adeyemi ya kashe matar mai suna Rachel Ayanwale ne bayan yaudararta cewa zai kai ta zuwa wajen addu’a a garin Awe kusa da garin Oyo inda ofishinta yake. “Bayan samun rahoton kisan gillar da aka yi wa matar da bacewar motarta Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama Adeyemi Morenikeji a Sango-Ota a Jihar Ogun,” in ji Kwamishinan wanda ya kara da cewa, “A binciken da suka gudanar kan mutumin sun gano cewa ya taba yin aiki a matsayin direban mijin matar inda ya sallame shi ba tare da biyansa albashin wasu watanni ba.”
Adeyemi Morenikeji ya ce, “Gaskiya ce na yi aiki a matsayin direban mijin matar wanda ya kore ni daga aiki ba tare da biyana albashin wasu watanni ba. Wannan ne ya sa na ji haushi na yaudari matarsa zuwa wani wuri na makure wuyanta da karfin tsiya don kada kururuwarta ya ankarar da masu wucewa har ta mutu na jefar da gawarta cikin daji na yi awon gaba da motarta, don sayarwa a garin Sango-Ota inda asirina ya tonu aka kama ni.”
Da aka tambaye shi me ya jefa shi cikin wannan hali? Sai cikin kuka ya ce, “Rashin kyakkyawar tarbiyya daga mahaifina tun ina da kuruciya ce ta jefa ni shiga cikin miyagun yara na koyi irin wadannan abubuwa.”