Dan fashin da aka yi wa afuwa ya kashe dan banga a Zariya
Wani matashi da aka taba yanke wa hukunci kan fashi da makami, amma aka yi masa afuwa ya kashe wani dan banga da ke kokarin shiga tsakani kan zargin da ake yi masa na satar waya a Zariya, Jihar Kaduna. Matashin mai suna Ibrahim Idris wanda ake wa lakabi da Ibrahim Wayes, dan kimanin shekara […]

Wani matashi da aka taba yanke wa hukunci kan fashi da makami, amma aka yi masa afuwa ya kashe wani dan banga da ke kokarin shiga tsakani kan zargin da ake yi masa na satar waya a Zariya, Jihar Kaduna.
Matashin mai suna Ibrahim Idris wanda ake wa lakabi da Ibrahim Wayes, dan kimanin shekara 22 yana zaune ne a Unguwar Rafin Sidi, Hanwa a karamar Hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna.
Aminiya ta ziyarci Unguwar Rafin Sidi, aka kashe dan bangar kuma dan agajin kungiyar Jama’atu Nasril Islam mai suna Suleiman danjumai mai shekara 30, wanda ke zaune a Unguwar Rafin Sidin.
Yayan marigayin, Malam Abdullahi Muhammadu ya shaida wa wakilimu cewa “A ranar Juma’ar da ta gabata, dan uwana Suleiman ya rasa ransa a yunkurin yin sulhu. Wanda ya kashe mana dan uwa, kanen Mai unguwarmu ne. Ana zarginsa da shiga dakin wani yaro mai suna Yahaya ya dauke masa waya, kuma ya gane wayar tasa a hannun shi barawon. Sai ya ce wannan wayarsa ce, shi kuma wanda ake zargi da satar wayar ya karyata.”
Ya ce, “Yahaya ya kai kara wurin ’yan banga domin su shiga tsakani, sai ’yan bangar suka fara bincike. Da suka gamsu cewa waya ta Yahaya ce, sai suka ce Ibrahim ya kawo waya. Har ma ’yan sanda sun zo sai ’yan bangar suka ce za a yi sulhu. Amma daga bisani wanda ake zargin ya saci wayar ya ki kawo ta. Don haka ranar Juma’a bayan Magariba sai marigayin ya je gidan wanda ake zargi ya sa ci wayar domin ya karbo ta. Ashe ya fito da wuka a boye a hannunsa, yana fitowa kawai sai ya daba wa marigayin a kirji, a gefensa na dama. Nan take ya fadi kasa, jini ya barke sai aka kwashe shi zuwa asibiti, kafin a kai asibiti ya rasu.”
Binciken Aminiya ya gano cewa matashin da ake zargi da kisan dan bangar, bai dade da fitowa daga gidan yari ba, domin mako uku ke nan da fitowarsa, a dalilin afuwar da aka yi masa, da sunan rage cinkoso a gidajen yari, wanda Babban Jojin Jihar Kaduna ke yi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu ya tabbatar da faruwa lamarin, ya ce, “Da ma wanda ake zargi da kisan kan mai suna Ibrahim Wayes ’yan sandan sun taba kama shi da laifin fashi da makami, inda su aka kai shi kotu aka yanke masa hukuncin zama gidan yari. Masu yi wa mutane afuwa na gidajen yari ne suka sako shi. To, yanzu kuma aka kara kama shi da zargin kisan kai. Muna bincike a yanzu kuma da zarar mun gama za mu gabatar da shi a gaban alkali.”
Game da korafin da ake samu cewa bayan afuwa ga masu aikata irin wannan mugun laifi, aikata laifuffukan sun karu, inda mutanen wurare daban-daban suka hadu da matsalolin tsaro, ko wane mataki ’yan sanda za su dauka domin magance faruwar haka a nan gaba?
ASP Mukhtar ya ce, “Akwai shirin da muke yi na gabatar da rahoto a wajen taron Majalisar Tsaro ta Jiha da ake yi a duk mako, domin taron ya shafi masu ruwa-da-tsaki a harkar tsaro; domin daga lokacin da aka yi aikin rage cinkoso a gidajen yari mako uku da suka wuce, mun samu irin wannan matsalar har kusan kashi uku daga wurare daban-daban kuma duk wadanda aka yi wa afuwar ne suka haifar da matsalolin.”