dan fim Jim Iyke zai auri Nadia Buari?

Kamar yadda ake ta yawo da bayanin cewa dan wasan fim Jim Iyke yana soyayya da abokiyar aikinsa da ke kasar Ghana, Nadia Buari, labarin ya zama tsohon yayi, domin kuwa a yanzu batun aure ake cewa zai tabbata a tsakaninsu.Masu gani su gaza kyalewa sun dade suna bin kadin ’yan wasan biyu, inda suka […]

dan fim Jim Iyke zai auri Nadia Buari?

Jim Iyke da Nadia BuariKamar yadda ake ta yawo da bayanin cewa dan wasan fim Jim Iyke yana soyayya da abokiyar aikinsa da ke kasar Ghana, Nadia Buari, labarin ya zama tsohon yayi, domin kuwa a yanzu batun aure ake cewa zai tabbata a tsakaninsu.
Masu gani su gaza kyalewa sun dade suna bin kadin ’yan wasan biyu, inda suka tabbatar da cewa babu wani taro da zai faru a farfajiyar nishadantarwa, ba tare da masoyan sun halarta tare ba, madamar an gayyaci daya daga cikinsu. Kamar yadda wani ma ya bayyana: “Ko a kwanakin baya da Jim Iyke ya gudanar da bikin kaddamnar da shirinsa na talabijin mai taken ‘Unscripted’ a Legas, Nadia ta halarci wurin kuma ta taka muhimmiyar rawa, a matsayinta na budurwar mai bikin.
Haka kuma, a kwanakin baya da aka shiga Facebook ana yada maganar cewa an ganta da sabon saurayi ba Jim ba, Nadia ta shiga turakarta ta karyata batun, ta ce har yanzu soyayyarsu da Jim Iyke tana nan daram, kuma suna shirin zama miji da mata.
Sai dai kuma a wani bayanin da aka samu daga bakin jami’in hulda da jama’a na dan wasa Jim, Mitch Nagaman, ya shaida wa kafar watsa labarai ta Intanet, Nigeriafilms cewa ba gaskiya ba ne cewa akwai batun soyayya tsakanin Jim Iyke da Nadia Buari. “Yan wasan biyu ba su tafiyar da wata soyayya tsakaninsu, abin da ke tsakaninsu bai wuce zumunci da alakar aiki ba kawai.” Inji shi.
Sai dai wani dan jaridar intanet a Ghana, Meyawa Debrah ya bayyana cewa babu shakka akwai soyayya tsakanin Jim da Nadia, musamman yadda ya ce lokacin da aka gabatar da bikin mawaka na Ghana, ’yan jaridar hoto sun yi ta maida hankalinsu ga masoyan biyu, wadanda aka rika gani tare da juna a ko’ina. Koma dai yaya ta kasance, lokaci zai tabbatar da abin da ake boyewa na batun aure ko a’a.