Dan fim Lee Thompson Young ya kashe kansa

An samu tabbacin cewa dan wasan nan na kamfanin fina-finai na Disney da ke Amurka, Lee Thomson Young ya halaka kansa, a lokacin da aka tsinci gawarsa a yashe, a gidansa da ke birnin Los Angeles da ke Amurka.Manajan Lee ta fuskar hulda da ’yan jarida ne ya tabbatar da haka ga mujallar TMZ, inda […]

Dan fim Lee Thompson Young ya kashe kansa

Marigayi Lee Thompson YoungAn samu tabbacin cewa dan wasan nan na kamfanin fina-finai na Disney da ke Amurka, Lee Thomson Young ya halaka kansa, a lokacin da aka tsinci gawarsa a yashe, a gidansa da ke birnin Los Angeles da ke Amurka.
Manajan Lee ta fuskar hulda da ’yan jarida ne ya tabbatar da haka ga mujallar TMZ, inda a wata takardar sanarwa ya ce: “Tare da bakin ciki nake sanar da cewa Lee Thompson Young ya kashe kansa a safiyar yau din nan. Lee dai dan wasa ne mai fikira, ga shi cike da kuruciya. dan wasa ne mai kayatarwa. Babu shakka za a dade ana kewarsa.”
dan wasa Lee, wanda ya fito a fim din kamfanin Disney mai suna “The Famous Jett Jackon,” an samu gawarsa ce a Litinin din da ta gabata a gidansa, wacce ke dauke da alamun harbin bindiga, wanda ake kyautata zaton shi ya harbi kansa da kansa. Kafin mutuwarsa, shekarunsa 29 da haihuwa.
Ya zuwa rubuta labarin nan dai, har yanzu ba a samu dalilin da ake jin ya sanya dan wasan ya kashe kansa ba, kodayake ’yan sanda na ci gaba da bincike.