dan fim Saheed Balogun zai maka tsohuwar matarsa kotu

dan fim din nan na Kudancin Najeriya, Saheed Balogun ya yi barazanar maka tsohuwar matarsa Fathia Balogun kotu madamar ta ci gaba da amfani da sunansa.Kamar yadda bayanai suka gabata, dan wasan ya rabu da matar tasa ne shekaru kadan da suka gabata, kuma ya yi alkawarin zai haramta mata amfani da sunansa a tare […]

dan fim Saheed Balogun zai maka tsohuwar matarsa kotu

dan fim din nan na Kudancin Najeriya, Saheed Balogun ya yi barazanar maka tsohuwar matarsa Fathia Balogun kotu madamar ta ci gaba da amfani da sunansa.
Kamar yadda bayanai suka gabata, dan wasan ya rabu da matar tasa ne shekaru kadan da suka gabata, kuma ya yi alkawarin zai haramta mata amfani da sunansa a tare da nata, sai dai an samu labarin cewa har yanzu Fathia tana amfani da sunan tsohon mijin nata, inda ake kiranta da sunan ‘Fathia Balogun.
Kamar yadda Saheed ya ce: “Ita tsohuwar matata ce, batun sunana da har yanzu take amfani da shi kuwa, ya kusa zuwa karshe, domin kuwa dokar Najeriya ta nuna cewa bayan kun rabu da matarka zuwa shekara uku ko hudu, za ka iya daukar matakin hana ta amfani da sunanka. Idan har ita tana son ci gaba da amfani da sunana, to idan na auri wata kuma fa, wane suna za ta yi amfani da shi? Don haka bukatar ta daina amfani da sunana, ba yana nufin ina fada da ita ba ne.”
A kwanakin baya, an ji Fathia tana bugun gaba, tana cewa babu wanda ya isa ya hana ta amfani da sunan. Sai dai wata majiya ta ce tsohon mijin nata har ma ya riga ya shigar da kara kotu, domin ya nemi a hana ta amfani da sunan nasa. Sai dai ita kuma ta sha alwashin babu wanda zai taka mata burki. Kamar yadda ta ce: “Ni abin ma yana ba ni dariya, domin kuwa sunana Fathia Balogun, kuma haka za a ci gaba da kira na da Balogun, babu wanda ya isa ya canja mani suna ko ya ce zai hana ni amfani da shi.