dan Fodiyo ne ya fara hade Najeriya wuri daya ba Turawa ba – Farfesa Yahaya
Fitaccen malamin jami’ar nan Farfesa dahiru Yahaya ya ce mujaddadi Shehu Usmanu dan Fodiyo ne ya hade masarautun Arewa da wasu yankunan tsakiyar Najeriya da a ke kira Middle Belt da wuri daya a matsayin masarauta dulkulalliya, gabanin hada Kudancin kasar nan da Arewa da a ke kira amalgamation da Turawan mulkin mallaka suka yi. […]

Fitaccen malamin jami’ar nan Farfesa dahiru Yahaya ya ce mujaddadi Shehu Usmanu dan Fodiyo ne ya hade masarautun Arewa da wasu yankunan tsakiyar Najeriya da a ke kira Middle Belt da wuri daya a matsayin masarauta dulkulalliya, gabanin hada Kudancin kasar nan da Arewa da a ke kira amalgamation da Turawan mulkin mallaka suka yi.
Farfesa dahiru Yahaya wanda malami ne a Jami’ar Bayero ta Kano ya bayyana haka ne a yayin gabatar da lacca a wurin bikin Ranar Shehu dan Fodiyo da aka gudanar Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.
Malamin wanda shi ne Babban Bako Mai jawabi a wurin bikin, ya tabo tarihin irin gwagwarmayar da Shehu dan Fodiyo da almajiransa suka yi, inda suka kwato wasu yankuna daga hannun sarakuna da ke mulki a lokacin sakamakon cuta da zaluncin da suke yi wa jama’arsu. Ya ce dan Fodiyo ya samu nasara ne sakamakon jajircewar da ya yi wajen tabbatar da adalci ga daukacin al’ummar yankunan ba tare da nuna bambancin kabila ba, inda ya ce mulki na tabbata a kan adalci koda babu addini, amma ba ya tabbata idan babu adalci, koda da addini.
A jawabin Babban Limamin Masallacin Unguwar ’Yan Majalisar, Sheikh Nuru Khalid ya bukaci shugabanni su yi adalci wajen gudanar da mulkin al’ummarsu.
Shugaban Cibiyar Bincike (Resource Forum) ta kungiyar ’yan uwa Musulmi reshen Abuja da ta shirya taron, Malam Yusha’u bin Sheikh, ya ce dandalinsu na shirya taron ne a Lahadin karshe na watan Safar a duk shekara, don yin bita a kan kyawawan ayyukan da Shehu Usman dan Fodiyo ya aiwatar don amfanar na baya.