dan Hadaddiyar Daular Larabawa ya yi majalisa a saman bishiyar dabino
Wani dan asalin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), mai suna Awad Harmoos AlMarzrouie ya yi wata hadaddiyar majalisa a saman bishiyar dabino. Saboda jin dadin wannan fadar bishiyar dabino, Awad har kira yake yi ga mutane cewa: “ku zama bakina a saman bishiya!” Kuma ta haka AlMazrouie ke saukar da bakinsa a fadarsa ta musamman a […]
Wani dan asalin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), mai suna Awad Harmoos AlMarzrouie ya yi wata hadaddiyar majalisa a saman bishiyar dabino. Saboda jin dadin wannan fadar bishiyar dabino, Awad har kira yake yi ga mutane cewa: “ku zama bakina a saman bishiya!” Kuma ta haka AlMazrouie ke saukar da bakinsa a fadarsa ta musamman a Hadaddiyar Daular Larabawa.
“Ina son nishadantar da bakina ta hanyar mai kayatarwa,” kamar yadda AlMazrouie ya bayyana wa jaridar Khaleej Times. “Tana nuni da wani yanayi na daban wajen saukar baki daura da dan iccen da muke matukar kauna, wato dabino,” inji shi.
Majalisar mai tsawon mita takwas, an yi ta ne da karfe, a yankin Liwa inda gona AlMazrouie take a Yammacin kasar. “sabuwar majalisata ta zama fada abin kauna ga daukacin iyalaina. A nan muke zama mu ci dabino,” a cewarsa.
Al Mazrouie’s two little children, Mohammed and Nasser, as well as his guests can easily climb up to the tree through a conbenient staircase, also made of iron.
‘’Ya’yan AlMazrouie biyu, Mohammed da Nasser, tare da bakinsa suna hawa wannan majalisar cikin sauki, ta kan wata matattakala da ke like jikin bishiyar, wadda ita ma aka kerata da karfe.
“Majalisar bishiyar dabinona, ita kadai nike da ita a halin yanzu, kuma zama abin sha’awa ga masu son dabino, har ma da ’ya’yana maza biyu da ’yan mata biyu.”
Bu Mohammed, wato lakabin mai majalisa, yana da shekara 35, ya ce babu wanda ya ba shi dabarar yin wannan majalisa. Don haka dai a cewarsa bai kwaikwayi kowa ba.
“Wannan tunani na ne, na kuma fara mafarkin yinta ne shekara uku da ta wuce,” ya fadi hakan ne a lokacin da yake sharhi game da wata matattakala da wani mutumin Saudiyya ya yi wa mahaifiyarsa, don ta samu sauki tsinko dabino, tamkar yadda ta saba yi a lokacin da take cikin koshin lafiya da karfinta.
Wannan majalisar saman dabino AlMazrouie ya kashe mata kudi har Dirhami dubu 15, wato daidai da Nairas miliyan guda da dubu 200. “Na shafe kwana 15 ina ginata a gonata, wadda ke cike da bishiyar dabinai guda 800.
Saboda kokarin kula da yake yi da gonar dabinonsa, AlMazrouie yana da nau’ukan dabinai 50 a gonarsa, wadda ya saba kara mata da zarar ya samun sababbin nau’uka. “Nau’ukan dabinon da suka fi shajhara a gonata su ne: Majdool da Al Dabbas da Al Barhi da Al Sukari da Al Sakei, Al Khneizi da Al Khalas,” inji shi.
Saboda kwarewarsa noman dabino, ya saba cin gasar dabino ta Liwa da ake gudanarwa kowace shekara. “Na samu matsayi na biyu a bana, inda nau’ukan dabinona Dabbas da Kheizi suka samar mini da Dirhami dubu 75,” inji shi.
Al Mazrouie dai yana zaune ne a Yammacin birnin Zayed, ya ce yana tunanin gina irin wadannan majalisu ko fadoji a saman dabinai. “Ina son fito da sabon fasali ko kirkiro sabon abu, wadanda ke da tushe a al’adarmu, sannan suka dace da zamani.