dan hakin da ka raina…
Labudda, hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke, wanda ya warware tsigewar da Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta yi wa tsohon Gwamna, Murtala Nyako a makon jiya ya nuna rashin dacewar amincewa da ayyukan gadarar shugabanni kai tsaye, da kuma irin zabin da masu kokarin dagewa wajen ganin an kamanta gaskiya da adalci ke kasancewa, […]
Labudda, hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke, wanda ya warware tsigewar da Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta yi wa tsohon Gwamna, Murtala Nyako a makon jiya ya nuna rashin dacewar amincewa da ayyukan gadarar shugabanni kai tsaye, da kuma irin zabin da masu kokarin dagewa wajen ganin an kamanta gaskiya da adalci ke kasancewa, ko kuma biye wa masu son biye zuciya don biyan bukatarsu.
Shi dai Murtala Nyako tun da farko an zarge shi ne da karya wasu dokoki da ka’idoji har guda 20, wadanda suka hada da bayar da kwangiloli ba bisa kaidojin da aka gindaya don yin haka ba da kuma kwashe wasu Naira miliyan 300 daga cikin tulin dukiyar talakawan jihar, ta yin amfani da wani kamfani mai suna Hydro Source Resources don gina wata hanyar motar da ta zagaya ta bayan garin Mubi da kuma wuce gona da iri wajen kauce wa ka’idojin aikinsa ta yin amfani da ‘yanuwa da abokan arziki wajen yin amfani da wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati don arzurta kansa. Da kuma facakar da ta janyo salwantar wasu kudi kusan Naira miliyan dubu 12, tsakanin shekarun 2012 da kuma 2013, ta hanyar yin amfani da ofishin sakataren gwamnatinsa.
‘Yan majalisun dokokin Jihar Adamawa guda 19, cikin 26 ne suka sanya hannu a batun tsige shi.; Daga bisani kuma bayan gwamnatin tarayya ta shiga al’amarin, ta yi ruwa, ta kuma yi tsaki, sai aka ci gaba da yada farfaganda game da zargin da aka yi wa Murtala Nyako har hakan ya kara bata shi a idanun talakawan Jihar Adamawa, wadanda suka dage lallai bai kamata a bari ya sha da wadancan laifuffukan da aka zarge shi da aikatawa ba. Hakan ne kuma ya sa aka dauki wani matakin da mutane da yawa suka gani haramtacce ne, don tsige Nyako a lokacin. An samu nasarar kawar da shi a watan Julin shekarar 2014. Tun daga wancan lokacin ne kuma Murtala Nyako ke ta yin fafitika, ko kuma a ce aikin Baban Giwa, a banza don neman komawa bisa mukaminsa. Kotun daukaka kara ta ki ta komar da shi bisa kujerarsa ta gwamna, ganin cewa, wa’adinsa na gwamna ya kare. Ana dai iya cewa an yi amfani ne da wani kuskure wajen daukar matakan tsige shi, aka warware hukuncin majalisar dokokin Jihar Adamawa na tsige shi, amma ba bisa bahasin da aka bi ba na tabbatar da wadancan zarge-zarge guda 20 da aka yi masa ba.
Matsalar da ta sa batun tsigewar ta dada yin kamari ta taso ne sa’ilin da Murtala Nyako ya soki lamirin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda kuma ya zarge shi da kokarin wargazawa da kuma gurgunta yankin Arewacin kasar nan ta hanyar bullowa da yin amfani da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram. Wannan ita ce hujjar da aka tabbatar ta kara ruruta wutar tsige Murtala Nyako. Haka nan kuma ana iya cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Cif Rotimi Amaechi ya tsallake rijiya da baya yayin da tsohon Shugaba Jonathan ya nemi a tsige shi saboda katobarar da ya yi irin ta Nyako. Hakan kuwa ya faru ne saboda dagewar da ‘yan Majalisar jiharsa suka yi wajen ba shi cikakken goyon baya don tsira daga sharrin masu neman ganin bayansa. Abin mamaki game da yadda ‘yan majalisun jihar Ribers suka agazawa Cif Amaechi shi ne yadda kuma a halin yanzu suka fi kowa babatu game da wajibcin bin doka da oda a Jihar Ribas, game da Gwamna Nyesom Wike, babban dan adawa da Rotimi Amaechi. Ai al’amarin duniya yau gare ka ne, gobe kuma ga waninka. To, idan kuwa haka ne yaya tsohon Shugaba Jonathan ke ji a zuciyarsa yanzu haka, musamman yadda aka yi ta zargin cewa, shi ne ya takura wa su Nyako da Amaechi, ya kuma dage lallai sai ya ga bayansu?
A halin yanzu ba zai so a ce za a yi masa yadda ya yi masu ba, kuma shi ma zai dage lallai sai an bi doka da oda idan har da a za a ce Shugaba Muhamadu Buhari zai zargo shi don amsa wasu zargin laifuffukan da ake zaton ya aikata.
A zamanin mulkin tsohon Shugaba Olusegun Aremu Obasanjo ma ya taba yin katsalandan a cikin harkokin shari’ar da ake yi a kotuna da kuma matakan da majalisun dokoki ke dauka game da batun tsittsige tsoffin gwamnonin Jihar Pilato, Chief Josha dariye da kuma marigayi Cif Diepreye Alamieyeiseigha na Jihar Bayelsa da kuma Rashid Ladoja na Jihar Oyo. Sa’ilin da Dariye da Ladoja suka tsallake rijiya da baya, shi kuwa Alamisieyeeigha ruwa ya ci shi, domin ba wanda zai tsamo shi. Haka nan aka tsige shi ba da laifinsa ba, aka kuma sanya Turawan Ingilishi suka ci amanarsa, har sai da ya yi shigar burtu kafin ya tsere daga kasar, duk da haka nan kuma bai tsira ba, sai da aka tsige shi bayan gudowarsa daga kasar da aka cafke shi, aka dankwafar da shi gaban shari’a.
Amma sai dai duk da yadda tsohon Shugaba Aremu Obasanjo ya kokarta don tsige wadancan gwamnonin, hakarsa ba ta cimma ruwa ba, domin kundin tsarin mulki bai ba shi sararin yin haka ba. Muddin dai ba an samu hadin kai tsakanin madafun iko guda uku na kasar nan ne ba, to fa ba ta yadda za a iya tsere wa yunkurin shugabanni na yin amfani da dokoki wajen karya doka da oda. Babu wanda zai iya yin nasara idan ya yi wa doka kama-karya, ko hawan kawara, kamar yadda shari’ar Nyako ta nuna. Kauce wa doka da oda ba zai iya yiwuwa ba idan mabiya sun zuba wa shugabanni idanu da nufin taka musu burki idan sun yi niyyar hakan. Dokokin kasar nan dai ba su ware kowa ba, suka hana shi yin amfani da su. Tilas kowa da kowa ya bi doka, ya kuma san cewa doka da oda suna gaba da kowa, kuma ko an ki, ko an so, za a yi hukunci da su a kan kowa, ciki har da wanda yake ganin shi ya fi karfin kowa. Yanzu dai wadanda suka yi kutungwilar tsige Nyako bisa kujerar Gwamna sai su saduda, domin sun gane cewa, ‘dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido.’