Dan hidimar kasa ya mutu a hadarin kwalekwale
Wani kwalekwale ya kife da wani mai yi wa kasa hidima NYSC a Guji Dam jihar Bauchi, Joseph Adebayo. Dan hidimar kasar dai zai kammala yi wa kasa hidima ‘yan kwanaki masu zuwa. Adebayo dai dan jihar Ogun wanda ya kammala karatunsa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ilaro. Kwalekwalen ya kife ne lokacin da […]
Wasu matasa masu yi wa kasa hidima lokacin karbar horo a sansaninsu.
Wani kwalekwale ya kife da wani mai yi wa kasa hidima NYSC a Guji Dam jihar Bauchi, Joseph Adebayo.
Dan hidimar kasar dai zai kammala yi wa kasa hidima ‘yan kwanaki masu zuwa.
Adebayo dai dan jihar Ogun wanda ya kammala karatunsa a kwalejin kimiyya da fasaha ta Ilaro. Kwalekwalen ya kife ne lokacin da Adebayo yake kokarin tsallake ruwan.
Sufeton shiyyar NYSC, Mahadi Habila Sada ne ya sanar da rasuwar dan hidimar kasar.