dan Hisba ya datse yatsun manomi a Jigawa

Wani dan Hisba a karamar Hukumar Kaugama da ke Jihar Jigawa ya sanya gatari ya datse yatsun hannun wani manomi saboda zarginsa da yi masa barna a gona. dan Hisban wanda ’yan sanda suka kama shi tuni suka gurfanar da shi a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse domin yi masa shari’a.Da […]

dan Hisba ya datse yatsun manomi a Jigawa
dan Hisba ya datse yatsun manomi a Jigawa

Wani dan Hisba a karamar Hukumar Kaugama da ke Jihar Jigawa ya sanya gatari ya datse yatsun hannun wani manomi saboda zarginsa da yi masa barna a gona. dan Hisban wanda ’yan sanda suka kama shi tuni suka gurfanar da shi a gaban Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse domin yi masa shari’a.
Da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Ustaz Aliyu Galamawa kan lamarin, ya ce ba su da masaniya a kan labarin amma za su bincika kuma
da zarar sun kammala bincike a kan wanda ake tuhumar za su bayyana wa
manema labarai matsayin hukumar kan wanda ake tuhumar.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Yahaya Yayari ya ce ba za su bayyana sunan wanda ake tuhumar ba sai sun kammala bincike a kan lamarin.