Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusuf Ladan ya rasu
Kwararren dan jarida Alhaji Yusuf Ladan Dan Iyan Zazzau ya rasu yana da shekara 86
Allah Ya yi wa Alhaji Yusuf Ladan, Dan Iyan Zazzau rasuwa bayan fama da rashin lafiya.
Alhaji Yusuf Ladan ya rasu a gidansa da ke Kaduna safiyar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2020 yana da shekara 86 a duniya.
- Sai da muka biya N6.6m kafin a saki ’ya’yanmu —Iyayen ’yan mata 26
- An halasta shan giya da zina bayan yi wa Shari’ar Musulunci kwaskwarima a UAE
Za a yi sallar jana’izarsa bayan sallar Azahar a Masallacin Juma’a na Maiduguri Road, Kaduna.
A lokacin rayuwarsa, Marigayi Alhaji Yusuf Ladan ya kasance fitaccen dan jarida, tsohon Manajan
Daraktan Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin na Jihar Kaduna (KSMC), kuma Hakimin Kabala.