“Dan Kare”
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe, da fatan ana cikin Koshin lafiya A yau na kawo muku labarin ‘Dan Kare.’ Labarin ya yi nuni ne kan illar rashin bin maganar iyaye. A sha karatu lafiya. Taku: Amina Abdullahi Akwai wata karya wadda take da ’ya’ya masu yawa. Karyar tana zaune ne a gonar wani manomi. Manomin […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe, da fatan ana cikin Koshin lafiya A yau na kawo muku labarin ‘Dan Kare.’ Labarin ya yi nuni ne kan illar rashin bin maganar iyaye. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Akwai wata karya wadda take da ’ya’ya masu yawa. Karyar tana zaune ne a gonar wani manomi.
Manomin yana kiwon wadannan karnukan ne domin su taya shi gadi a cikin gonarsa.
A cikin gonar akwai wata rijiya wadda karyar ta gargadi ’ya’yanta a kan yin wasa kusa da ita gudun kada su fada.
Ran nan daya daga cikin ’ya’yan karyar ya yanke shawarar zuwa ganin rijiyar wadda a cewarsa, yana son ganin yadda cikin rijiyar yake.
Yana leKa rijiyar sai ya hango mai kama da shi amma bai san cewa inuwarsa ce ba. Daga nan sai ya shiga yin hauhi, sai ya lura na cikin rijiyar ma yana haushi.
Abin ya ba shi haushi, sai kawai ya tsunduma cikin rijiyar don ya hadu da wancan karen.
A nan ya gane kurensa, lokacin da ya ji shi a cikin ruwa shi kadai. Nan ya riKa haushi har manomi ya ji ya ciro shi da wata igiya.
Tun daga ranar ya riKa bin umarnin iyayensa sau da Kafa.
Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi daga wannan labari.