Dan kasar Kenya ya mutu bayan ya fado daga saman filin wasan Qatar
John Njau Kibue ya fado ne daga saman filin wasan tare da jin mummunan rauni wanda hakan ya yi ajalinsa.
Wani mai gadi dan kasar Kenya, ya mutu bayan da ya fado daga saman ginin filin wasannin motsa jiki na Lusail da ke kasar Qatar.
Masu shirya Gasar Cin Kofin Duniya da ke ci gaba da gudana yanzu haka a kasar ta Qatar sun ce sun soma gudanar da bincike kan mutuwar John Njau Kibue mai shekara 24.
- Kotu ta tsare masu gadi 2 a kurkuku kan satar katifun makaranta
- Peter Obi ya dage gangaminsa na jihohin Ekiti da Ondo
Bayanai sun ce marigayin ya ji rauni sosai sakamakon fadowar da ya yi daga saman ginin a ranar Asabar, jim kadan bayan da kasar Argentina ta lallasa Croatia a wasan na kusa da karshe.
Rahotanni daga yankin sun ce, tawagar ba da agajin gaggawa ne suka fara duba marigayin bayan faruwar hatsarin, kafin daga bisani aka dauke shi zuwa Asibitin Hamad inda a nan rai ya yi halinsa a ranar Talata.
Masu shirya gasar sun ce sun sanar da ‘yan uwan marigayin abin da ya faru, tare kuma da ba su tabbacin za su mika duk wani hakkin marigayin ga ‘yan uwansa.