Dan kasar Sin ya ciro hakarkarinsa ya yi abin wuya

Wani dan kasar Sin, mai suna He Yunchang, mai shekara 48, ya ciro hakarkarinsa, ya yi wa kansa abin wuya, don kwalliya a wajen wasa. Wannan dan wasa, wanda gwanin zayyana ne, ya sha yin kwalliya da jininsa, inda ya bayyana wa manema labarai cewa yana yin wadannan al’amura masu wuya a rayuwa ne, domin […]

Dan kasar Sin ya ciro hakarkarinsa ya yi abin wuya
Dan kasar Sin ya ciro hakarkarinsa ya yi abin wuya

 He-Yunchang, wanda ya yanka kansa, ya ciro kashin hakarkari ya yi abin wuyaWani dan kasar Sin, mai suna He Yunchang, mai shekara 48, ya ciro hakarkarinsa, ya yi wa kansa abin wuya, don kwalliya a wajen wasa. Wannan dan wasa, wanda gwanin zayyana ne, ya sha yin kwalliya da jininsa, inda ya bayyana wa manema labarai cewa yana yin wadannan al’amura masu wuya a rayuwa ne, domin ya nuna ’yancin kansa.
A ranar  8 ga watan ga Augustar 2008, lokacin da kasar Sin ta yi bikin bude gasar wasan Olemfik, sai ya rataya abin wuyansa, wanda kusan rabinsa na zinare ne, rabi kuwa kashin hakarkarinsa ne.
Ya ce wannan al’amari nasa, yana yi ne don ya nuna ‘’yancin kansa,’ domin a cewarsa, yana iya daukar wa kansa duk abin da ya yanke hukunci a kansa, duk da cewa akwai abubuwan da suka fi karfinsa.
“Akwai mutane masu karfin hali a cikin al’umma, wadanda ra’ayinsu kan zama ra’ayin sauran mutane, sannan akwai dokokin zamantakewa wadanda ke tankwara al’umma,” kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, a dakin shirya kwalliya da adonsa da ke wajen garin birnin Beijing, yana magana da kakkausar murya, yana ta bankar taba, inda akalla yake zukar karan taba 120 a kowace rana.
daya daga cikin ayyukan da ya gudanar kwanan nan shi ne, ya shafe kunbarsa da jini a kafafu da hannaye, inda ya kwarara launin jin a daukacin yatsunsa 10.
“Manufata ita ce, jin zafi da farko na da fa’ida, sannan samun kariya al’amari ne mai muhimmanci na biyu. Duk da haka nakan yi kokarin shawo kan matsalolina. Muhimmin al’amari dai ba ni bari in mutu,” inji shi.
dimbin hotunansa da zanensa da gumakan da ya yi duk ana sayar da su a daukacin fadin Turai da Amurka.
Ya taba tara mutum 25 a shekarar 2010, don su tantance masa kan cewa ko zai ji zafi idan aka yi masa tiyata da wuka, ba tare da an yi masa allurar kashe zafin ciwo ba. Masu kuri’ar jin ra’ayi sai suka karke da daukar hotuna tare da shi. Shi kuwa ya kwanta a tube aka yanka shi jini ya yi ta zuba.
“He Yunchang masanin kimiyyar sarrafawa da karya lagon zafin ciwo ne,” a cewar Judith Nelson, shugabar wajen baje kolin kayan zayyana da zane-zane na White Rabbit Gallery da ke Sydney, babban birnin Austiraliya.