dan kasuwa ya boye almajiri tsawon wata 2 yana lalata da shi a Suleja
Wani dan kasuwa da ke gudanar da sana’ar sayar da bulawus a yankin Maje na garin Suleja da ke Jihar Neja, Malam Hassan Muhammad ya fada komar ’yan sanda a sakamakon zargi da ake yi masa na jikkata wani yaro mai shekara 14 ta hanyar yi masa luwadi a shagonsa, inda suke kwana tare.Yaron mai […]
Wani dan kasuwa da ke gudanar da sana’ar sayar da bulawus a yankin Maje na garin Suleja da ke Jihar Neja, Malam Hassan Muhammad ya fada komar ’yan sanda a sakamakon zargi da ake yi masa na jikkata wani yaro mai shekara 14 ta hanyar yi masa luwadi a shagonsa, inda suke kwana tare.
Yaron mai suna Harisu Musa, wanda almajiri ne da malaminsa ya dauko daga karamar Hukumar bagwai ta Jihar Kano zuwa garin Lambata da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna, kamar watanni takwas da suka gabata, yanzu haka ana kula da shi a Babban Asibitin Suleja, a sakamakon matsalar ciwon ciki da yake fuskanta bayan kumbura da cikin ya yi da kuma rashin yin tafiya daidai.
A ganawarsa da Aminiya, almajirin wanda ya share sama da wata biyu a wajen mutumin, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya dauko shi ne daga garin Lambata, inda yake karatun allo, bayan ya shaida masa cewa zai taimaka masa ta hanyan ajiye shi a wajensa suna yin kasuwanci tare. Ya ce daga nan ne kuma ya nuna masa motarsa da yake zirga-zirgar zuwa kasuwannin kauye da ita; inda suka wuce zuwa wata kasuwar a ranar, kafin daga bisani suka koma garin Maje da dare suka kwana a shagonsa.
Ya ce a cikin daren, bayan farkawarsa, ya samu kansa ba tare da wando ba, sannan a lokaci guda ya ga mutumin a kusa da shi yana share najasa a jikinsa da kyalle.
“Da gari ya waye na yanke shawarar barin shagon amma bayan ’yar tafiya kadan sai na ji kamar ba na cikin hayyacina ga shi kuma ina jin jiri. Hakan ta sa na dawo wajensa na ci gaba da zama tare da shi.” Inji shi.
Ya ce mutumin yakan kulle shi a shagon a duk lokacin da zai je kasuwar kauye ko kuma garin Suleja, inda yake sarin kaya. Ya kara da cewa, yakan yi masa luwadi kamar sau biyu a mako, kuma yana samun sauki ne kawai daga ciwon cikin, idan suka hadu.
Da yake bayani a kan al’amarin, malamin yaron mai suna Malam Muhammad Tasi’u, cewa ya yi, ’yan kwanakin kadan gabanin Babbar Sallah da ta gabata, wasu daga cikin almajirai da suka taho daga yanki guda da yaron, sun tafi gida don yin bikin tare da iyayensu bayan iyayen sun amince da su je. Ya ce sai dai shi yaron tare da wasu yaran ba su samu izinin tafiyar ba daga wajen iyayensu, kasancewar ba su cika shekara guda da rabuwa da su ba.
Ya ce ana cikin hakan sai suka rasa ganin yaron ana kwana guda gabanin Sallah. “Na bincika can gida ko an gan shi amma babu labarinsa. A sakamakon hakan sai na je wajen iyayensa bayan ’yan kwanaki, inda na karfafa masu gwiwa tare da neman su ci gaba da addu’a kamar yadda mu ma muke yi a nan. Bayan sama da wata biyu da bacewarsa, sai wasu abokaina da ke karantarwa a yankin Maje suka kira ni ta waya a ranar Juma’ar da ta gabata; inda suka sanar da ni cewa an gane yaron bayan jami’an tsaro, ’yan banga sun sanar da su.”
Babban ofishin ’yan banga na masarautar Suleja da ke yankin su ne da farko suka kama wanda ake zargin, bayan wasu da ke makobtaka da shi sun tsargu da yanayin zamansa da yaron, kafin daga bisani suka mika shi ga babban ofishinsu na Suleja. Majiyar Aminiya a ofishin ta tabbatar da cewa mutumin wanda dan asalin garin Wurno ne da ke Jihar Sakkwato, inda matansa na aure da ’ya’yansa bakwai ke da zama, ya amince da aikata al’amarin bayan kawo shi wajensu. Daga nan ne kuma suka mika shi ga babban ofishin ’yan sanda na yanki da ke garin Suleja a ranar Asabar da ta gabata, inda ake ci gaba da bincike a kan al’amarin.
Wani jami’in jinya na Babban Asibitin Suleja ya ce tuni suka fara yi wa yaron jinya kuma suna jiran wasu sakamakon gwaji da aka yi masa, ciki har da na HIb, don sanin abin da yake ciki.