dan kasuwa ya halaka kansa da wuka
A safiyar ranar Talatar da ta gabata ce mazauna unguwar Sheka, a karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano suka wayi gari da alhinin rasuwar wani dan kasuwa mai suna Alhaji Ado Mai Siminti, inda ya halaka kansa.Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya fito kofar gidansa, inda kai tsaye ya wuce wurin da ake sayar da nama, […]
A safiyar ranar Talatar da ta gabata ce mazauna unguwar Sheka, a karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano suka wayi gari da alhinin rasuwar wani dan kasuwa mai suna Alhaji Ado Mai Siminti, inda ya halaka kansa.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya fito kofar gidansa, inda kai tsaye ya wuce wurin da ake sayar da nama, ya dauki wukar ya yanka makogwaronsa da ita.
Wani wanda abin ya faru a kan idonsa, Ali Muhammed ya bayyana cewa ya ga lokacin da marigayin ya je wurin da ake sayar da naman ya tsaya. “Muna daga wani kofar gida muna hira, na ga lokacin da Mai Siminti ya fito daga gidansa ya je ya tsaya a wurin da ake sayar da nama. Zuwa can sai muka hango ya dauki wuka ya kara ta a wuyansa. Hakan ya sa wasu daga cikinmu suka yi kukan kura suka nufe shi don hana shi aiwatar da abin da ya yi niyya. Duk kokarin da suka yi na su kwace wukar daga hannunsa abin bai yiwu ba, kasanceawr ya rike wukar katakau. Daga nan ya shige gidansa a guje ya bar samarin da raunuka a hannuwansu. Da ya shiga gidan ma sai ya wuce bandaki ya kulle kansa ya aiwatar da abin da ya kudurci aikatawa. A nan mutane suka yi kokarin balle kofar bandakin; inda suka shiga suka same shi kwance cikin jini.”
Aminiya ta kalato cewa lokacin da jami’an ’yan sanda suka zo suka dauke shi don kai shi Asibitin kwararu na Murtala Muhammed, suna kan hanya ya mutu. Daga nan suka karasa asibitin, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Majiyar Aminiya ta rawaito cewa akwai jita-jitar da ke yawo, cewa marigayin ya dauki wannan mataki a kansa ne sakamakon bashi da ya yi masa yawa.
Marigayin ya rasu ya bar matan aure biyu da kuma ’ya’ya da dama. Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Wanann dai shi ne karo na uku a ’yan makonnin da ba su wuce takwas ba, ake samun mutane suna daukar hukuncin kashe kawunansu. A kwanan baya ma an samu irin haka a Unguwar Na’ibawa, Kano, inda wani mutum ya kashe kansa ta hanyar yankar makogwaronsa tare da yanke mazakutarsa gaba daya. Haka kuma an samu wani mutumin da ya kashe kansa a mayankar Kano.
ASP Magaji Musa Majiya ya tababtar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunarsu ta fara bincike don gano musabbabin rasuwar marigayin.