Dan kasuwa ya rataye kansa a Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na cewa wani dan kasuwa ya hallaka kansa ta hanyar rataya a cikin shagonsa da ke kan titin Gidan Zoo cikin kwaryar birnin Kano. Mutumin wanda kafin halaka kan nasa, yake gudanar da kasuwancin siyar da tayoyi da batiran mota, an same shi ne a mace bayan makwabta da ’yan santa […]

Dan kasuwa ya rataye kansa a Kano

Shagon da aka tsinci gawar mutum a ciki

Rahotanni daga Jihar Kano na cewa wani dan kasuwa ya hallaka kansa ta hanyar rataya a cikin shagonsa da ke kan titin Gidan Zoo cikin kwaryar birnin Kano.

Mutumin wanda kafin halaka kan nasa, yake gudanar da kasuwancin siyar da tayoyi da batiran mota, an same shi ne a mace bayan makwabta da ’yan santa sun balle shagon.

Shaidu sun ce mamacin ya halarci sallar La’asar tare da Jama’a da misalin karfe 4, inda bayan idar da sallah kowa ya koma shagonsa ya ci gaba da sabgogin kasuwancinsa.

A kan hanyarsa mamacin ta komawa shagonsa, sai ya tsaya a shagon makwabcinsa ya karbi igiya ya tafi.

An rawaito cewa, isarsa shagonsa ke da wuya, sai ya tura dansa na cikinsa da suke zama a shagon tare koyaushe ya siyo masa abinci da wasu da wasu kayan da yake bukata a wani wurin.

Fitar yaron ke da wuya, kafin ya dawo shagon mahaifin nasa ya rataye kansa.

Lokacin da yaron ya dawo shagon bayan ya siyo abubuwan da ya aike shi ya tarar da shagon a rufe.

Ya dan jira na dan wani lokaci yana zaton za a bude sai ya fara tunanin ina mahaifinsa yake, ina ya shiga?

Ana cikin haka ne makwabcin da mahaifin ya karbi igiya a wurinsa ya shiga tunani da zargin cewa bayan mamacin ya karbi igiyar shi ya rufe kansa a shagon.

Ana bude shagon sai aka tarar da shi a mace, wuyansa daure da igiya, ya rataye da kansa.

Har yanzu Rundunar ’Yan Sandan Jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano