Dan Katsina ya yi na uku a gasar karatun Kur’ani ta duniya
Dan asalin Jihar Katsina mazaunin Unguwar Inwala dake cikin garin Katsina mai suna Abdulganiyu Aminu ɗan shekara 23 ne ya samu nasarar zama na uku a gasar haddar Al-kur’ani hizifi 60 mai tajweedi a gasar wadda aka yi kwanaki uku ana yi a Kasar Saudiyya. Gasar wadda kasashe 30 daga cikin 82 da suka halarta […]
Dan Katsina ya yi na uku a gasar karatun Kur’ani ta duniya
Dan asalin Jihar Katsina mazaunin Unguwar Inwala dake cikin garin Katsina mai suna Abdulganiyu Aminu ɗan shekara 23 ne ya samu nasarar zama na uku a gasar haddar Al-kur’ani hizifi 60 mai tajweedi a gasar wadda aka yi kwanaki uku ana yi a Kasar Saudiyya.
Gasar wadda kasashe 30 daga cikin 82 da suka halarta suka samu nasarar fafatawa a gasar karatun Alkur’ani Mai Tsarki na bana, wanda ya gudana a Masallacin Manzon Allah (SAW) dake birnin Madina. Masu gasa 115 ne suka fafata a matakai hudu na gasar da aka aiwatar wato; Haddar Alkur’ani hizifi 60 da Tafsiri da kuma hizifi 60 da Tajweed da hizifi 30 da kuma hizifi 5.
Shugaban Kwamitin Shirya Gasar na Jahar Katsina, wanda kuma shi ne Babban Alkalin jahar, Mai Shari’a Musa Danladi ya yi wa wakilinmu karin haske kan yadda aka yi har dan Jahar Katsina ya wakilci Najeriya a wannan gasa ta Duniya.
Ya ce, “Bayan kammala gasar a matakin ƙasa, Allah Ya sa wannan yaro shi ne ya zo na daya a wannan mataki na Tajweed. To da ma akwai Gidauniyar Sarki Abdul’aziz wadda a wannan karon shekaru 36 kenan tana daukar wannan nauyi na Musabakar karatun Kur’ani Mai Tsarki ta Duniya.
“Kuma duk shekara ana dauko wadanda suka zamo na farko a ƙasashensu a wadannan bangarori biyu, wato hadda mai tafsiri da kuma tajweedi. To kamar yadda aka saba, a bana an nemi a tura wadannan masu gasa ta hanyar aikowa Jami’ar Danfodiyo. Jahar Katsina muke da mai tajweed,” Inji shi.
Shugaban ya kara da cewa, bayan samun waccan takardar gayyata, sai Mai Girma Gwamnan Jaha, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce, ba za a bar yaron ya tafi shi kadai ba, “saboda haka aka nada wakillan da zasu tafi tare da shi. Mai shari’a Musa Danladi ya cigaba da cewa, ni na jagoranci tagawar da ta hada da Kwamishinan Harkokin Addini na Jaha, Mai ba Gwamna shawara ta fuskar Ilmi mai zurfi tare kuma da daya daga cikin alkalan gasar na duniya wanda yake shi ma dan jahar Katsina”.
Haka shi ma gwarzon da ya zo na uku, Abdulganiyu ya shaidawa Aminiya cewar ya fara shiga gasar tun daga 2009 a matakan da suka fara da na karamar hukuma har zuwa na jaha a 2016. “Na samu shiga na ƙasa a 2017 bayan na zamo na farko a jaha. A garin Ilorin ne muka yi na ƙasa inda na yi na biyu. A shekarar 2018 na yi na daya a matakin kasa na hardar Kur’ani hizifi 60 da Tajweedi, wanda aka yi anan Katsina.
“Wannan nasara ce ta bani damar zuwa gasar duniya wadda aka yi a Madina, na kuma yi na uku. Mu biyu ne muka samu wannan matsayi iri daya, wato ni da Abdulkadir Mu’ammar Muftah Kindi dan Kasar Libiya”.
Kamar yadda Abdulganiyu ya ce, wannan zuwa gasar ya bashi damar yin aikin Umra da kuma ziyarar wurare da dama wadanda kowane musulmi yake da burin zuwa. Sai dai ya kara da jan hankali akan baiwa sha’anin addini fifiko fiye da komai, ba ma kamar wajen karatun Alkur’ani Mai Girma.
Sauran waɗanda suka yi nasara a sassan gasar sun hada da Ibrahim Abdullahi Abdulkadir As-Sa’awi ɗan Kasar Saudiyya, wanda ya zamo na daya a bangaren haddar Kur’ani hizifi 60 mai tafsiri da kuma dan Kasar Jordan mai suna Malik Adanan Subahi Usman, wanda ya zo na biyu. Sai kuma Amiru Yunusa Guru ɗan Jahar Bauchi wanda ya wakilci Najeriya a wannan bangaren ya zo na uku. Sai kuma bangaren haddar hizifi 60 da tajweedi, inda Haysam Sofar Ahmad ɗan Kasar Kenya ya zo na daya da Ubaidu Ma’an Abdulsalam Furaihan daga Jordan ya zo na biyu, sai shi Abdulganiyu Aminu ɗan Jahar Katsina wanda ya wakilci na Najeriya a wannan bangare ya zo na uku.