dan kunar bakin wake ya hallaka a Potiskum

Wani dan kunar bakin wake da ake zaton dan kungiyar Boko Haram ne ya hallaka kansa tare da ji wa mutum rauni a lokacin da ya yi yunkurin kai hari ga wata cibiya ta mabiya Shi’a a garin Potiskum da ke Jihar Yobe. Wani da ke kusa da wurin da lamarin ya faru da ya […]

dan kunar bakin wake ya hallaka a Potiskum
dan kunar bakin wake ya hallaka a Potiskum

Wani dan kunar bakin wake da ake zaton dan kungiyar Boko Haram ne ya hallaka kansa tare da ji wa mutum rauni a lokacin da ya yi yunkurin kai hari ga wata cibiya ta mabiya Shi’a a garin Potiskum da ke Jihar Yobe.

Wani da ke kusa da wurin da lamarin ya faru da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa
Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:35 na yamma lokacin da dan kunar bakin waken ya yi yunkurin shiga rumfar da ’yan uwa Musulmin ke lazimi, sai dai kafin ya cimma burinsa sai bam din da ke jikinsa ya tashi da shi ya mutu.
An taba kai irin wannan hari a wannan cibiya a yayin hidimar karamar Sallar da ta gabata inda aka kashe mutum shida.
Da Aminiya ta tuntubi shugaban kungiyar ’yan uwa Musulmi na Potiskum, Malam Mustafa Lawan Nasidi kan lamarin ya ce dan kunar bakin waken ya yi yunkurin kai hari a Sakafa amma Allah Ya tsayar a kansa sai dai ya ji wa wasu mutum shida raunuka an kai su babban asibitin Potiskum.
Garin Potiskum a baya ya yi fama da hare-haren bam inda kusan ya fi kowane gari a Jihar Yobe fuskantar hare-haren ’yan bindiga.