Dan kunar-bakin-wake ya kashe mahaifinsa da mutum tara a masallaci
Wani dan kunar-bakin-wake jiya ya kai hari wani masallaci a jihar Borno lokacin sallar asuba inda ya tayar da bam din da ke jikinsa inda ya kashe kansa da sauran masu ibada tara har da mahaifinsa tare da yi wa saura munanan raunuka. An ce wanda ake zargin, dan kungiyar boko haram ne […]

Wani dan kunar-bakin-wake jiya ya kai hari wani masallaci a jihar Borno lokacin sallar asuba inda ya tayar da bam din da ke jikinsa inda ya kashe kansa da sauran masu ibada tara har da mahaifinsa tare da yi wa saura munanan raunuka.
An ce wanda ake zargin, dan kungiyar boko haram ne kuma ya kai harin masallacin da ke kusa da gidan mahaifinsa da ke unguwar Abuja a garin Gamboru ya kashe masu ibada.
Wanda ya tsira daga harin Muhammadu Mustapha ya ce sun kirga gawarwaki 11 da gawar dan kunar-bakin-wake da ta mahaifinsa.