dan kunar bakin wake ya so dana bam a Damaturu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai harin kunar bakin wake da wani da ake kyautata zaton mamba ne na kungiyar Boko Haram ne mai suna Abubakar Sadik Umar mai shekara 19 ya so kaiwa da wata motar a kori kura kirar Chebrolet a ofishin ’yan sanda na A Dibision […]

dan kunar bakin wake ya so dana bam a Damaturu
dan kunar bakin wake ya so dana bam a Damaturu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai harin kunar bakin wake da wani da ake kyautata zaton mamba ne na kungiyar Boko Haram ne mai suna Abubakar Sadik Umar mai shekara 19 ya so kaiwa da wata motar a kori kura kirar Chebrolet a ofishin ’yan sanda na A Dibision da ke tsakiyar garin Damaturu.  
Da yake bayani ga manema labarai kan yunkurin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Alhaji Sunusi A. Rufa’i ya ce, dan kunar bakin waken ya yi yunkurin kai harin ne da misalin karfe 8.40 na safiyar ranar Lahadin da ta gabata, inda ya tuko motar dauke da abubuwa masu fashewa ya nufo ofishin, inda take jami’an ’yan sandan da ke tsaronsa suka farga suka yi harbi sama, dan kunar bakin waken ya tsorata ya tsaya, kuma ya yi yunkurin gudu kafin su kama shi.
Kwamishinan ya ce, lokacin da jami’an suka fara tuhumarsa ya ce lallai motar na dauke da bama-bamai, inda aka same shi da sundukan iskar gas biyar da agogon bango da aka dana lokacin tashin baman da shi da sauran abubuwa masu hadari inda kwararru suka warware su.
Alhaji Rufa’i ya ce shi dan kunar bakin waken ya tabbatar musu cewa shi mamba ne na kungiyar Boko Haram kuma an turo shi ne daga yankin Talala a karamar Hukumar Damboa a Jihar Borno. “Ya ce kama shi aka yi aka sa shi cikin wannan kungiya da karfi, haka a lokacin da aka turo shi yin wannan aika-aika sai da aka rufe masa idanunsa sai da suka kawo garin Goneri a karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe aka sun ce masa tare da ba shi motar da kuma umarnin ya zo don aikata hakan.