dan kunar bakin wake ya tada bam a tashar motar Potiskum
Wani dan kunar bakin waken ya kai hari a tashar mota ta wajen garin da ke kan hanyar Potiskum zuwa Bauchi inda ya yi halkaka mutum biyar duk da wanda ya kai harin. Wani da ke kusa da tashar motar da lamarin ya faru da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa […]
Wani dan kunar bakin waken ya kai hari a tashar mota ta wajen garin da ke kan hanyar Potiskum zuwa Bauchi inda ya yi halkaka mutum biyar duk da wanda ya kai harin.
Wani da ke kusa da tashar motar da lamarin ya faru da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa maharin ya tada bam din da yake dauke da shi ne da misalin karfe 10:35 na safiyar Lahadi yayin da fasinjoji ke kokarin shiga mota zuwa Bauchi da Jos a kusa da wani gidan mai.
Ya ce, lokacin da bam din ya fashe sai da ya dauki misalin minti biyar bai san halin da yake ciki ba.
Ya kara da cewa da kura ta lafa ya ga gawarwakin mutane a warwatse da wasu mutane a kwakkwance kafin mutane su rika daukar mutanen da suka jikkata zuwa asibiti.
Wani mai aiki a tashar Malam Ali ya bayyana wa Aminiya cewa, mutumin ya shammace su ne domin suna matukar kula da fasinjojin da ke shige da fice a tashar.
Ya ce faruwar lamarin ya sanya tilas za su kara tsaurara matakan da tsaro da suka dace don kiyaye lafiyar jama’a kuma ya roki fasinjojin su rika hakuri da sababbin matakan da za su iya gani domin za su yi ne domin kare lafiyarsu.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin babban jami’in ’yan sandan Potiskum kan faruwar lamarin hakarta ba ta cimma ruwa ba.