dan kwallon Madrid Jese ya gama kwallonsa a kakar wasa ta bana

A ranar Talatar da ta wuce ne dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid da ke Sifen ya gama kwallonsa a kakar wasa ta bana bayan ya ji mummunan rauni a kokon gwiwarsa ta dama a wasa zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da Champions […]

dan kwallon Madrid Jese ya gama kwallonsa a kakar wasa ta bana
dan kwallon Madrid Jese ya gama kwallonsa a kakar wasa ta bana

A ranar Talatar da ta wuce ne dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid da ke Sifen ya gama kwallonsa a kakar wasa ta bana bayan ya ji mummunan rauni a kokon gwiwarsa ta dama a wasa zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da Champions League a tsakanin Madrid da kulob din Schalke 04 da ke Jamus.
Tuni kocin kulob din Carlo Ancelotti ya tabbatar da wannan labari jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin Madrid da Shalke 04 bayan Madrid ta yi nasara da ci 3-1.
Jese Rodrigue dan kimanin shekara 21 ya samu matsala ne minti biyar kacal da fara wasa al’amarin da ya sa aka fitar da shi a kan makara kuma aka wuce da shi asibiti.