dan kwallon Madrid yana rokon Najeriya ta gayyace shi don ya yi mata kwallo
Wani matashin dan kwallo mai suna Derik Osede Prieto da yanzu haka yake buga wa kulob din Real Madrid na matasa da ke Sifen kwallo ya nuna sha’awar yi wa kasar haihuwarsa Najeriya kwallo a duk lokacin da aka gayyace shi. Derik, wanda ya shafe shekaru da dama a kulob din Madrid ya ce ya […]
Wani matashin dan kwallo mai suna Derik Osede Prieto da yanzu haka yake buga wa kulob din Real Madrid na matasa da ke Sifen kwallo ya nuna sha’awar yi wa kasar haihuwarsa Najeriya kwallo a duk lokacin da aka gayyace shi.
Derik, wanda ya shafe shekaru da dama a kulob din Madrid ya ce ya ki yarda ya buga wa Sifen kwallo ne, saboda kwadayin da yake da shi na yi wa Najeriya wasa.
Derik dai ya buga wa Sifen kwallo a matakin matasa a lokuta da dama amma bai taba yi wa babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar wasa ba, kuma hakan ce ta ba shi damar ya buga wa Najeriya kwallo a matakin manya a duk lokacin da aka gayyace shi kamar yadda dokar kwallo ta Hukumar FIFA ta shimfida.
dan kimanin shekara 22, Derik dai yana buga kwallo ne a matsayin mai tsaron baya na tsakiya (Central Defence) kuma yana da yakinin zai taimaka wa kungiyar Super Eagles a duk lokacin da aka gayyace shi.
Ya ce mahaifinsa dan Najeriya ne amma shi haifaffen Sifen ne don haka yake da zabin yi wa Sifen ko Najeriya kwallo a matakin manya.