Dan kwallon Najeriya Brown Ideye ya sayi motar Naira miliyan 45 a Ingila
Dan kwallon Najeriya Super Eagles da yanzu haka yake kwallo a kulob din West Brom na Ingila Brown Ideye ya sayi sabuwar motar yayi kirar 2015 Rolls Royce Ghost II da aka kiyasta kudinta a kan Dala dubu 250 kwatankwacin Naira miliyan 45.Labarin sayen motar Ideye ya fito fili ne bayan da abokinsa na kut-da-kut […]

Dan kwallon Najeriya Super Eagles da yanzu haka yake kwallo a kulob din West Brom na Ingila Brown Ideye ya sayi sabuwar motar yayi kirar 2015 Rolls Royce Ghost II da aka kiyasta kudinta a kan Dala dubu 250 kwatankwacin Naira miliyan 45.
Labarin sayen motar Ideye ya fito fili ne bayan da abokinsa na kut-da-kut da shi ma dan kwallon Najeriya ne da ke buga kwallonsa a Fotugal mai suna John Ogu ya sanar a kafar sadarwa ta Twitter a karshen makon jiya.
Sayen motocin gagari a wajen ’yan wasa ba sabon abu ba ne, don a shekarar bara sai da dan kwallon Kamaru Samuel Eto’o ya sayi motar da aka kiyasta kudinta a kan Naira miliyan 60. Su kuwa shahrarrun ’yan kwallon duniya irin su Cristiano Ronaldo an ruwaito suna hawa motocin garari ne da kudinsu ya haura Naira miliyan 100.