Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda
Abubakar Lawal mai shekaru 29 daga Jihar Sakkwato, ya rasu ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda

Marigayi Abubakar Lawal. (Hoto: @viperssc).
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda.
Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya rasu ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda.
Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene.
Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers Sports Club da ke kasar, inda ya fara wasa tun watan Yulin shekarar 2022, kafin nan ya shekara biyu yana taka lelda a kungiyar AS Kigali da ke kasar Rwanda.
- Luwadi: Magijanci ya lalata dan shekara 5 a Zariya
- Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700
- Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu
Kungiyar Vipers ta sanar Abubakar ya rasu ne a ranar Litinin bayan da ya fado daga hawa na uku da kataferen kantin mai suna Voicemall Shopping Arcade a Kampala.
A sakon ta’aziyyarta, kungiyar ta bayyaan marigayin a matsayin, “mutumin kirki mai kyakkyawar zuciya, mai yawan kyauta ne da kuma taimaka wa jama’a,” kamar yadda ya wallafa a shafinta na X.
Runudar ’yan sandan ta sanar da fara bincike kan musabbabin mutuwar dan kwallon na Najeriya.
Hukumar ’yan sandan Uganda ta bayyana cewa dan wasan ya gamu da ajalinsa ne a lokain da ya kai wa wata kawarsa ’yar kasar Tanzaniya ziyara a rukunin ginin.
A sakon ta’aziyyar dan wasan, kungiyar Nasarawa United, tsohuwar kungiyar Abubakar, ta ce, “Muna jimaminin mutuwar fuju’ar tsohon dan wasanmu Abubakar Lawal, kuma muna rokon Allah Ya sada shi da rahama.”
Shi kuwa Mustafa Kizza, dan wasan Uganda, ya ce: “Rashin Lawal abu ne mai wuyar jurewa. Mutumin kirki ne mai fara da hazaka da ba za mu taba mantawa da shi ba.“