Dan kwallon Najeriya ya suma saboda tsananin zafi

Dan kwallon gaban Kamaru Joel Tagueu ya kamu da ciwon zuciya kuma tuni mahukunta kulob din suka mayar da shi gida don a yi masa jinya. A binciken da daya daga cikin likitocin kulob din Dokta William Ngatchou  ya yi a kan Joel ne ana gab da wasan da Kamaru za ta buga da Guinea-Bissau […]

Dan kwallon Najeriya ya suma saboda tsananin zafi

Joel dan kwallon Kamaru da ya kamu da matsalar zuciya

Dan kwallon gaban Kamaru Joel Tagueu ya kamu da ciwon zuciya kuma tuni mahukunta kulob din suka mayar da shi gida don a yi masa jinya.

A binciken da daya daga cikin likitocin kulob din Dokta William Ngatchou  ya yi a kan Joel ne ana gab da wasan da Kamaru za ta buga da Guinea-Bissau a ranar Talatar da ta wuce a  gasar cin Kofin Afirka da ke gudana a kasar Masar aka gano dan kwallon yana dauke da matsalar ciwon zuciyar.

Kamaru a shafin sadarwarta ta shaida wa duniya ba za ta yi kasadar amfani da dan kwallon a gasar ba, saboda hadarin da ke tattare da yin haka ganin komai zai iya faruwa inda masu irin wannan matsala ke mutuwa ana tsakiyar wasa.

Joel dan shekara 25 yana buga kwallo ne a kulob din Maritimo da ke Potugal, kuma yana daga cikin zaratan ’yan wasan Kamaru a gaba.

Jim kadan bayan Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru (FA) ta  sanar da cire sunan dan kwallon daga jerin wadanda za su fafata a gasar sai hankalin magoya bayan kungiyar ya tashi.

Hukumar FA ta Kamaru daga ta nemi Hukumar CAF ta ba ta izinin maye gurbin Joel kuma tuni ta amince mata da haka.

Sai dai duk da rashin Joel, Kamaru ta fara gasar da kafar dama inda ta lallasa Guinea-Bissau da ci 2-0 a wasanta na farko.

Idan za a tuna Kamaru ce mai rike da kofin  bayan ta doke Masar da ci 2-1 a 2017 wanda hakan ya sa ta dauki kofin sau biyar a tarihi.