dan Majalisa ya raba wa dalibai 60 tallafin kudin karatu a Gombe

dan majalisar tsara dokoki daga Jihar Gombe mai wakiltar Mazabar Gombe ta Kudu a zauren Majalisar Dokokin jihar, Alhaji Mohammed Ahmed Bello, Sarkin Arewan Bolari, ya bai wa dalibai 60 daga mazabar sa tallafin karo karatu. dan majalisar ya bayar da wannan tallafin ne ga dalibai a karkashin Gidauniyar da ya kafa mai suna Sarkin […]

dan Majalisa ya raba wa dalibai 60 tallafin kudin karatu a Gombe
dan Majalisa ya raba wa dalibai 60 tallafin kudin karatu a Gombe

dan majalisar tsara dokoki daga Jihar Gombe mai wakiltar Mazabar Gombe ta Kudu a zauren Majalisar Dokokin jihar, Alhaji Mohammed Ahmed Bello, Sarkin Arewan Bolari, ya bai wa dalibai 60 daga mazabar sa tallafin karo karatu.

dan majalisar ya bayar da wannan tallafin ne ga dalibai a karkashin Gidauniyar da ya kafa mai suna Sarkin Arewa Bolari Foundation da zimmar tallafa wa ’ya’yan marasa galihu.
Kowanne dalibi ya samu tallafin Naira dubu 10-10 ne, wanda adadin kudin ya kai Naira dubu 600.
Alhaji Mohammed Ahmed Bello, ya ce wannan gidauniya ta sa ya kafata ne domin cika irin alkawuran da ya daukar wa al’ummar mazabar sa na cewa, ‘muddin suka zabe shi ya zama Mamba, wanda zai wakilce su a zauren majalisar dokokin jihar zai dinga bai wa ’ya’yan marasa galihu tallafin karo karatu.
“Wani bangare na alkawuran da na daukar wa jama’a ta lokacin yakin neman zabe na, shi ne, na cewa, zan ba da tallafin karo karatu ga daliban makarantun gaba da Sakandare, tunda na ci zabe, hakan ya sa bayan na ci zabe da ’yan watanni yanzu na ce zan cika wannan alkawarin,” inji Sarkin Arewan Bolari.
Ya ce wannan kyauta ya yi ta ne domin amfanar daliban jami’o’i da kwalejojin ilimi da suke gudanar da karatunsu a halin yanzu, irin su jami’a mallakar jihar da jami’ar gwamnatin tarayya ta Kashere da kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Gombe, da ma sauran manyan cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan.
Alhaji Mohammed Ahmed Bello, ya ci gaba da cewa a saninsa wadannan dalibai an zabo su ne bisa ga kokarinsu da kuma kasancewar su ‘ya’yan marasa galihu wasu kuma jiga-jigan jam’iyyar su ta APC ne suka zabo su, amma su din ma ’ya’yan marasa galihu ne.
Daga nan sai ya ce wannan gidauniya tasa, za ta ci gaba da ba da irin wannan tallafi da nan gaba yake sa ran bai wa dalibai 100 idan Allah ya wuce masa gaba, ta hanyar samun kudin da zai gudanar da ita.
Sannan sai Sarkin Arewan Bolarin, ya ce wannan gidauniya tasa ta Sarkin Arewa Foundation, ta gama dukkan shirye-shiryen ta wajen kaddamar da shirin ta na tallafa wa mata da matasa a bangarori daban-daban.