Dan Majalisa ya rasu a Jihar Kogi
Marigayi Hon. Enema Paul wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ya rasu ne a Abuja a taba ranar Asabar.
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kogi, mai wakiltar Mazaɓar Dekina 11, Honorabul Enema Paul ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi Hon. Enema Paul wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ya rasu ne a Abuja a taba ranar Asabar.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Aliyu Umar Yusuf ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar bayan fama da rashin lafiya.