dan Majalisa ya tallafa wa matasa da matan aure

dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Arewa, Kangiwa, Dandi, Kamba Alhaji Ibrahim Bawa Kamba ya rarraba Keke-NAPEP ashirin ga matasan yankin ya kuma ba manoma injinan ban-ruwa, yayin da ya ba mata injinan nika da kekunan dinki.Alhaji Ibrahim Bawa kamba ya fada wa Aminiya cewa kafin wannan ya giggina asibitoci da makarantu kuma kwanan nan […]

dan Majalisa ya tallafa wa matasa da matan aure
dan Majalisa ya tallafa wa matasa da matan aure

dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Arewa, Kangiwa, Dandi, Kamba Alhaji Ibrahim Bawa Kamba ya rarraba Keke-NAPEP ashirin ga matasan yankin ya kuma ba manoma injinan ban-ruwa, yayin da ya ba mata injinan nika da kekunan dinki.
Alhaji Ibrahim Bawa kamba ya fada wa Aminiya cewa kafin wannan ya giggina asibitoci da makarantu kuma kwanan nan zai kara rarraba injinan nika 380 ga mata da Keke-NAPEP 20 ga matasa da kekunan dinki 300 ga matan aure, domin magance rashin aikin yi da matsa ke fama da shi.
Game da rade-radin cewa yana sha’awar takarar Gwamnan Jihar Kebbi ganin fosta-fostansa sun cika jihar, sai ya ce duk inda jama’arsa suka ce ya fito, to ba gudu ba ja da baya koda wane ne za su kara da shi.
Alhaji Ibrahim Kamba ya kuma ce ayyukan da ya gudanar cika alkawari ne da ya yi wa al’ummar mazabarsa a lokacin yakin neman zabe.
Ya ce bayan da samar da asibitoci da makarantu da ba da injinan ban-ruwan da Keke-NAPEP da kekunan dinki, zai fito da wasu hanyoyin na inganta ci gaban al’ummar yankinsa da maza da mata da matasa za su kara amfana.