Dan Majalisar Dattawa Sanata Ben Uwajumogu ya mutu

Dan Majalisar Dattawa, Sanata Ben Uwajumogu mai wakiltar mazabar jihar Imo ta Arewa, ya mutu a safiyar yau Laraba a Abuja. Abokin aikinsa Sanata Rochas Okorocha, ne ya tabbatarwa manema labarai mutuwar Sanata Ben, inda ya ce Sanatan ya fadi ne a ban daki daga bisani aka kaishi asibitin unguwar Apo da ke Abuja. Cikakken […]

Dan Majalisar Dattawa Sanata Ben Uwajumogu ya mutu

Dan Majalisar Dattawa, Sanata Ben Uwajumogu mai wakiltar mazabar jihar Imo ta Arewa, ya mutu a safiyar yau Laraba a Abuja.

Abokin aikinsa Sanata Rochas Okorocha, ne ya tabbatarwa manema labarai mutuwar Sanata Ben, inda ya ce Sanatan ya fadi ne a ban daki daga bisani aka kaishi asibitin unguwar Apo da ke Abuja.

Cikakken rahoton na nan tafe.