Dan Majalisar Dokokin jihar Sakkwato ya rasu bayan fadi a Majalisar

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato Honarabul Isa Harisu Kebbe, mai wakiltar karamar hukumar Keɓɓe ya rasu a yau Litinin. Margayin ya yanke jiki ya fadi a zauren majalisa in da nan take aka samu ya rasu bayan an kai shi asibitin koyarwa na Usman Danfodiyo anan aka tabbatar da rasuwarsa. Isa Harisu, dan siyasa ne […]

Dan Majalisar Dokokin jihar Sakkwato ya rasu bayan fadi a Majalisar

Isa Harisu Kebbe

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato Honarabul Isa Harisu Kebbe, mai wakiltar karamar hukumar Keɓɓe ya rasu a yau Litinin.

Margayin ya yanke jiki ya fadi a zauren majalisa in da nan take aka samu ya rasu bayan an kai shi asibitin koyarwa na Usman Danfodiyo anan aka tabbatar da rasuwarsa.

Isa Harisu, dan siyasa ne mai kwazo ya rike mukamai da dama a gwamnatin jihar Sakkwato ciki har da mai bai wa gwamna shawara kafin ya shiga zauren majalisa, kwarewarsa a harkar mulki ya sanya jam’iyarsa ta APC ta nemi ya tsaya takarar kujerar mataimakin Kakakin majalisar dokokin jiha in da ya sha kasa hannun wanda ke rike da kujerar yanzu Aminu Magaji na jam’iyyar PDP.