dan Majalisar Filato ya tallafa wa makarantun Ittahadu

dan Majalisar Dokokin Jihar Filato mai wakiltar Jos ta Arewa maso Arewa, Alhaji Ibrahim Baba Hassan ya tallafa wa daliban makarantun kungiyar Ittihadu Anwaril Hidayat da yunifom.Da yake mika tallafin ga shugaban kungiyar ta Ittihadu, Alhaji Yusuf Yahaya a wurin taron tunawa da Ranar Isra’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW) da kungiyar ta shirya a […]

dan Majalisar Filato ya tallafa wa makarantun Ittahadu
dan Majalisar Filato ya tallafa wa makarantun Ittahadu

dan Majalisar Dokokin Jihar Filato mai wakiltar Jos ta Arewa maso Arewa, Alhaji Ibrahim Baba Hassan ya tallafa wa daliban makarantun kungiyar Ittihadu Anwaril Hidayat da yunifom.
Da yake mika tallafin ga shugaban kungiyar ta Ittihadu, Alhaji Yusuf Yahaya a wurin taron tunawa da Ranar Isra’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW) da kungiyar ta shirya a Jos, Alhaji Ibrahim Baba Hassan ya yi fata yunifom din da ya bayar zai kara karfafa gwiwar daliban kan karatun da suke yi.
dan majalisar wanda Alhaji Muhammad Shitu ya wakilta ya yi kira ga daliban su kara zage damtse wajen neman ilimi domin da ilimi ne duniya take ci gaba. “Mu kara tashi tsaye wajen neman ilimin addini da na zamani, idan muka samu ilimi za mu taimaki kawunanmu da mutanenmu da kasa baki daya,” inji shi.
Ya bayar da tabbacin cewa da yardar Allah zai ci gaba da taimaka wa matasan mazabar wajen neman ilimi.
A jawabin Babban Limamin Jos Sheikh Lawal Adam ya yi addu’ar fatan alheri ga dan majalisar kan tallafin da ya bai wa daliban makarantun kungiyar, tare da addu’ar Allah Ya kara daukaka kungiyar da makarantunta da dalibansu baki daya.
Babban Limamin wanda Na’ibinsa Sheikh Gazali Isma’ila Adam ya wakilta ya bayyana muhimmanci Isra’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW), inda ya ce Sahabban Manzon Allah (SAW) 25 ne suka ruwaito Hadisan wannan tafiya ta Isra’i da Mi’iraji saboda muhimmancinta.
Tun farko a jawabin shugaban kungiyar Ittihadu, Alhaji Yusuf Yahaya ya ce a bikin Maulidi na shekara uku da suka gabata ne, dan majalisar ya yi musu alkawarin ba su tallafin yunifom. Don haka ya mika godiyarsu ga dan majalisar kan wannan alkawari da ya cika.
Ya ce kungiyar ita ce take shirya maulidi a garin Jos kuma a yanzu ta kirkiro da gasar karatun hadisai da gasar kasida da taron Muharram da kuma taron tunawa da Isra’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW). “Shi Musulmi a rayuwarsa babu abin da yake kauna kamar Annabi Muhammad (SAW) don haka kungiyar nan ta kirkiro da taron tunawa da Ranar Isra’i da Mi’irajin Annabi Muhammad (SAW). Ya zama wajibi Musulmi su rika girmama wannan rana ta 27 ga watan Rajab wato ranar da Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) ya yi Isra’i da Mi’iraji saboda muhimmancinta,” inji shi.