dan Majalisar Shira ya ba mata 400 jarin naira dubu biyar-biyar

dan Majalisar Dokokin Jihar Bauci mai wakiltar mazabar Shira da Yana, karkashin Jam’iyyar APC Alhaji Awwal Hassan ya ba mata 400 jarin Naira dubu biyar-biyar kyauta saboda su ja jari don raya sana’o’i ko kasuwancinsu sakamakon gudunmawar da suke bayarwa a lokutan zabe.A jawabinsa a yayin raba kudin da ya shirya a garin Yana Alhaji […]

dan Majalisar Shira ya ba mata 400 jarin naira dubu biyar-biyar

dan Majalisar Dokokin Jihar Bauci mai wakiltar mazabar Shira da Yana, karkashin Jam’iyyar APC Alhaji Awwal Hassan ya ba mata 400 jarin Naira dubu biyar-biyar kyauta saboda su ja jari don raya sana’o’i ko kasuwancinsu sakamakon gudunmawar da suke bayarwa a lokutan zabe.
A jawabinsa a yayin raba kudin da ya shirya a garin Yana Alhaji Awwal Hassan ya ce ya ware sama da Naira miliyan uku domin raba wa matan aure da zawarawa da ’yan mata a matsayin tallafin raya sana’o’insu a gidajensu.
Yace ya yi haka ne saboda ya lura ana barin mata a baya duk da cewa su ne kan gaba wajen fita zabe, inda maza kawai ke cin gajiyar siyasar.
Ya ce a karon farko ya shirya ba mata 350 ne wannan taimako amma ganin akwai gundumomi da yawa ya kara zuwa 400, kuma nan gaba zai sake ba wasu matan.
A jawabin dan takarar Gwamnan Jihar Bauci a tsohuwar Jam’iyyar CPC, kuma jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Yusuf Maitama Tuggar ya yaba kokarin dan majalisar na gina makarantu da asibitoci da hanyoyi da kuma bayar da tallafi ga ’yan siyasa lamarin da a halin yanzu ya kawo kan matan yankinsa.
Ya ce a zaben 2015 suna da yakinin sanya tsintsiyarsu su share Jam’iyyar PDP daga fagen mulkin kasar nan da yardar Allah saboda gajiya da mulkinta da jama’a suka yi.
Cikin wadanda suka yi jawabi a taron akwai Sakataren APC na Jihar Bauci Dokta Adamu Dabo da wakilin shugaban jam’iyyar na kasa Kyaftin Bala Jibir da Alhaji Garban Balu Shira da sauransu.