dan Majalisar Tarayya ya sha da kyar a hannun matasan Katagum

Matasa a garin Azare hedkwatar sun ba dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Katagum daga Jihar Bauchi kashi a lokacin da ya ziyarci mazabarsa domin wasu hidimomi bisa zargin ya kaurace wa mutanen da suka zabe shi na tsawon lokaci.dan Majalisar Alhaji Awwal dahiru Saleh ya gamu da fushin matasan ne a ranar Asabar da ta […]

dan Majalisar Tarayya ya sha da kyar a hannun matasan Katagum
dan Majalisar Tarayya ya sha da kyar a hannun matasan Katagum

Matasa a garin Azare hedkwatar sun ba dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Katagum daga Jihar Bauchi kashi a lokacin da ya ziyarci mazabarsa domin wasu hidimomi bisa zargin ya kaurace wa mutanen da suka zabe shi na tsawon lokaci.
dan Majalisar Alhaji Awwal dahiru Saleh ya gamu da fushin matasan ne a ranar Asabar da ta gabata lokacin da ’ya’yan jam’iyyarsa t APC suka rutsa shi a cikin zauren taron da shugabannin jam’iyyar suka kira domin zama da shi saboda a nuna masa matsaloli da hadarin da yake fuskanta na kaurace wa yankin da sauran batutuwa.
Wata majiya da ke cikin zauren taron ta shaida wa wakilinmu cewa tun suna cikin taron matasa suka fara kwantsama masa zagi ta taga suna cewa a bar su su shako shi don su gyara masa mu’amalarsa da mutane, “kamar wasa lamarin ya fi karfin shugabannin inda daga bisani suka nemi tserar da shi amma aka kasa isa jikin motarsa,” inji majiyar.
Majiyar ta ce ganin hadarin da yake fusakanta sai Awwal dahiru Saleh ya kwaso kusan dukkan kudin da ke aljihunsa ya mika wa matasan, amma karbarsu ke da wuya sai suka dalla masa mari suka yi ta ba shi kashi suka kekketa masa sutura, kafin ’yan sanda su kai masa dauki su kubutar da shi.
Kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, Alhaji Bappa Tafida Misau ya shaida wa wakilinmu cewa ba su ji dadin abin da aka yi wa dan majalisar ba. Kuma ya roki dan majalisar ya gyara tafiyarsa koda ba ya son sake tsayawa takara ya yi abin da zai tsira da mutuncinsa da na jam’iyyar ta hanyar kyautata wa wadanda suka zabe shi da kuma ziyartar mutanensa don ya zauna da mutane lafiya.