Dan Majalisar Tarayyar Jigawa ya rasu

Honorabul Isa Dogon Yaro ya rasu ne a Abuja sakamakon rashin lafiya.

Dan Majalisar Tarayyar Jigawa ya rasu

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Garki da Babura daga Jihar Jigawa, Honorabul Isa Dogon Yaro ya rasu.

Honorabul Isa Dogon Yaro ya rasu ne a Abuja sakamakon rashin lafiya.

Honorabul Isa Dogon Yaro ya zama ɗan Majalisar Tarayya ne bayan kotu ta kwace takarar Honorabul Aminu Kanta kan zargin amfani da sunan bogi.

Dan Majalisar Wakilai Mohammed Bello El-Rufai ya sanar da rasuwar a cikin sakon da ya wallafa a Facebook.

Hakazalika Honorabul Philip Agbese, Mataimakin Shugaban Majalisa ma ya mika ta’aziyyarsa, yana mai cewa ana sa ran gudanar da jana’iza a ranar Juma’a