Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya rasu
Dan Majalisar Wakilan ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 39 a duniya
Dan Majalisar Tarayya wakilta Mazabar Cikin/Kajuru ta Jihar Kaduna, Ekene Abubakar Adams ya rasu.
Honorabul Ekene, wanda dan Jam’iyyar LP ne, ya rasu yana da shekaru 39.
Sanarwar ta Akin Rotimi Jr ya fitar ta tabbatar da rasuwar dan Majalisar a safiyar Talata.