Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC
Ya ce kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki.
A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar.
Dan majalisar ya bayyana cewa kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
Sai dai Shugaban Marasa Rinjaye, Kingsley Chinda (PDP) ya daga kara da cewa ko da yake dan majalisar na da hurumin sauya sheka, amm ya kamata a bi abin da doka ta tanada.
- An nada sabon Mataimakini Mai Tsawatarwa na Majalisar Tarayya
- Dalibai 179 sun kammala Digiri da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero