Dan Majalisar Wakilai na jihar Jigawa ya rasu a Dubai

Dan Majalisar Wakilan Tarayya da ke wakiltar mazabar Garki- Babura a jihar Jigawa karkashin jam’iyyar APC, Mohammed Adamu Fagen Gawo ya rasu. Daya daga cikin iyalan Dan Majalisar mai suna Mohammed Hadi Inuwa, ne ya sanarwa manema labarai rasuwar marigayin yau Talata a birnin Dubai da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Mohammed Adamu Fagen Gawo, […]

Dan Majalisar Wakilai na jihar Jigawa ya rasu a Dubai

Mohammed Adamu Fagen Gawo

Dan Majalisar Wakilan Tarayya da ke wakiltar mazabar Garki- Babura a jihar Jigawa karkashin jam’iyyar APC, Mohammed Adamu Fagen Gawo ya rasu. Daya daga cikin iyalan Dan Majalisar mai suna Mohammed Hadi Inuwa, ne ya sanarwa manema labarai rasuwar marigayin yau Talata a birnin Dubai da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Mohammed Adamu Fagen Gawo, ya rasu ne ya nada shekara 74. Ya rasu ne bayan jinyar rashin lafiyar kafa da yaje yi Dubai.

Dan Majalisar a yanzu haka yana wa’adinsa karo na biyu a matsayin Dan Majalisar Wakilan Tarayya daga jihar Jigawa.

Ya rasu ya bar mata daya da yara 10.