Dan Majalisar Wakilai na Kano, Mohammed Hassan, ya rasu

Kafin rasuwarsa, an gan shi a taro da aka gudanar a gidan Kwankwaso da ke Abuja

Dan Majalisar Wakilai na Kano, Mohammed Hassan, ya rasu

Allah Ya yi wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu/Warawa ta Jihar Kano, Hon. Barista Mohammed Hassan, rasuwa a ranar Juma’a a wani asibiti da ke Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Shugaban masu yada labaransa, Muhammed Yaro Daba, ya tabbatar da rasuwar a cikin wata sanarwa, inda ya ce za a gudanar da sallar jana’izar mamacin a gidansa da ke Abuja ranar Asabar da misalin karfe 2:00 na rana.

Daba ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya cancanci koyi, tare da roƙon Allah Ya jiƙan sa da rahma, Ya sanya a Aljanna Firdausi, kuma Ya ba iyalansa haƙuri jure wannan babban rashi.

Barista Hassan, wanda aka zaɓe shi a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar NNPP a shekarar 2023, ya sauya sheƙa tare da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zuwa Jam’iyyar ADC a ’yan kwanakin baya.

Kafin rasuwarsa, an gan shi a taro da aka gudanar a gidan Kwankwaso da ke Abuja.

Marigayin ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 18.