Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Bakori ya rasu a Saudiyya

Ya rasu a birnin Madinah.

Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Bakori ya rasu a Saudiyya

Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, Honorabul Dokta Ibrahim Aminu Kurami

Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina, Honorabul Dokta Ibrahim Aminu Kurami ya rasu a Saudiyya.

Hon. Dokta Ibrahim Aminu Kurami ya rasu ne a kasa mai tsarki yayin da ya je aikin umara.

Dan Majalisar ya rasu ne bayan ’yar gajeruwar rashin lafiya da ya yi a birnin Madina da misalin karfe 2:00 na daren Litinin din nan.

Idan ba ku manta. ba an yi zabi Dan Majalisar ne a shekarar 2020 bayan rasuwar tsohon dan majalisar Honorabul Abdurrazak Ismail Tsiga a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar.

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya

’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu a Sakkwato

Gwamnati za ta mayar da yara 5,000 makaranta a Jigawa