Dan Majalisar Wakilai, Suleiman Lere ya rasu
Dan majalisar ya rasu yana da shekaru 53 a duniya bayan gajeriyar jinya.
Majalisar Tarayya ta sake wayan gari da rashin daya daga cikin ’yan Majalisar Wakilai, a ranar Talata.
Hon. Sulaiman Lere, mai wakiltar Lere a Majalisar Wakilai, ya rasu bayan gajeriyar jinya a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, yana da shekara 53.
- Ma’aikatan shari’a sun garkame kotuna bayan fara yajin aiki
- Matasan da suka yi wa mace fyade suka kashe ta a Kwara sun shiga hannu
- Ambaliyar Indonesiya da East Timor ta hallaka mutum 157
- Dalibai biyar na Kwalejin Harkokin Noma ta Kaduna sun kubuta
Takwaransa mai wakiltar Kudancin Kaduna, Mukhtar Ahmed ne ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar ta wayar tarho.
Rasuwar Lere ita ce ta shida da aka yi na ’yan majalisa tun daga shekarar 2019.
Idan ba a manta ba, dan majalisar mai wakiltar Bassa a Arewacin Filato, Haruna Maitala ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata, ya rasu ya bar yaro da wasu.