dan majalisar ya bukaci a kawo karshen rikici a tsakanin al’ummar Taraba da Filato

dan Majalisar Mazabar Ibbi a Majalisar Dokokin Jihar Taraba Alhaji Abdulkarim Lawal ya bukaci gwamnatocin jihohin Taraba da Filato da Nasarawa da suke makwabtaka da juna su kira wani taro cikin gaggawa don nemo hanyar kawo karshen rashin zaman lafiya a yankunan iyakokinsu. dan majalisar ya bukaci haka ne a hirarsa da wakilinmu, inda ya […]

dan majalisar ya bukaci a kawo karshen rikici a tsakanin al’ummar Taraba da Filato
dan majalisar ya bukaci a kawo karshen rikici a tsakanin al’ummar Taraba da Filato

dan Majalisar Mazabar Ibbi a Majalisar Dokokin Jihar Taraba Alhaji Abdulkarim Lawal ya bukaci gwamnatocin jihohin Taraba da Filato da Nasarawa da suke makwabtaka da juna su kira wani taro cikin gaggawa don nemo hanyar kawo karshen rashin zaman lafiya a yankunan iyakokinsu.

dan majalisar ya bukaci haka ne a hirarsa da wakilinmu, inda ya ce ganin yadda ake yawan samun asarar rayuka da dukiya a yankin karamar Hukumar Ibbi sakamakon yadda ’yan bindiga daga yankin Jihar Filato ke cin karensu babu bababka, kuma hukuma ta kasa daukar wani mataki, ya zama tilas jihohin su dauki mataki cikin gaggawa.
Alhaji Lawal ya ce jama’ar yankin Ibbi masu yawan gaske sun kauracewa garuruwansu saboda tsoron hare-haren ’yan bindiga kuma ga ruwan sama ya sauka amma mutane sun kasa komawa don nome gonakinsu.
Ya yi zargin cewa ’yan kabilar Tarok daga Jihar Filato ne suka addabi jama’ar yankin amma saboda suna da uwa a murhu an kasa yin wani hukunci a kansu.
Alhaji Lawal ya ce ’yan bindigar sun kwace wasu kauyuka da suke cikin yankin Ibbi sun maida su a karkashin ikonsu a Jihar Filato amma hukuma ta kasa yin komai.
Alhaji Abdulkarim Lawal ya ce a kwanakin baya ’yan kabilar Tarok din sun yi wa sojoji kusan 10 kisan gilla suka kwace manyan makamai daga hannun sojojin amma saboda daurin gindi sai ga shi manyansu sun gudanar da zanga- zanga cewa ana cin mutuncin ’yan kabilarsu.
dan majalisar ya ce muddin gwamnatocin jihohin ba su zauna sun dauki mataki kan lamarin ba, to za a ci gaba da hallaka mutanen karamar Hukumar Ibbi.
Ya ce an taba zama tsakanin jam’an jihohin uku da wakilin hukumar kula da iyakoki ta tarayya aka fidda iyakar kowace jiha, amma sai ga shi ’yan kabilar Tarok sun tuge turakun da aka kafa da ke nuna iyakar kowace jiha, amma ba a dauki wani ba har zuwa yanzu.
Alhaji Abdulkarim ya ce al’ummarsa na fuskantar mawuyacin hali saboda yadda ’yan kabilar Tarok ke hallaka su.