dan Majalisar ya tallafa wa matan da suka rasa mazansu a Potiskum
dan Majalisar Tarayya daga mazabar Potiskum da Nangere a Jihar Yobe a karkashin Jam’iyyara PDP, Alhaji Sabo Garba ya kaddamar da wani shiri na rarraba kayayyakin tallafi ga mata zawarawa100 aksari wadanda suka rasa mazajensu sandadiyar rikicin Boko Haram da kuma matan da ke dauke da cutar kanjamau don yin sana’o’in dogaro da kai.Da yake […]
dan Majalisar Tarayya daga mazabar Potiskum da Nangere a Jihar Yobe a karkashin Jam’iyyara PDP, Alhaji Sabo Garba ya kaddamar da wani shiri na rarraba kayayyakin tallafi ga mata zawarawa100 aksari wadanda suka rasa mazajensu sandadiyar rikicin Boko Haram da kuma matan da ke dauke da cutar kanjamau don yin sana’o’in dogaro da kai.
Da yake rarraba tallafin a Potiskum Alhaji Sabo Garba ya ce mata sune suka fi fuskantar fadawa cikin halin wahalhalu iri-iri a sanadiyar rikicin BokoHaram saboda akasari sun rasa mazajensu tare da barinsu da yara marayu.
Ya ce don haka ya zama wajibi a tallafa musu domin ganin ba su sake fadawa cikin karin masifu ba sakamakon kalubalen rayuwa da ake ciki a yanzu.
Alhaji Sabo Garba ya ce, abin damuwa ne yadda ake tarar da matan suna yawo a kan tituna suna bara don ciyar da marayun da suke gabansu, inda ya ce hakan ba karamin kalubale ba ne ga shugabanni da kuma al’umma baki daya.
Wasu daga cikin kayayyakin da dan majalisar ya rarraba ga matan sun hada da kekunan dinki da kayayyakin yin sabulu da man shafawa da makamantansu.
Wata daga cikin matan da suka ci gajiyar tallafin, Malama Hauwa Muhammad ta bayyana wa Aminiya cewa, ta ji dadin tallafin keken dinki da aka ba ta, domin ta tabbata za ta taimaka mata a kokarin da take yi na kula da marayu uku da aka bar ta da su.