dan Majilisar Wakilai ya raba kayan tallafi ga jama’ar mazabarsa
Kayayyakin da suka hada da kekunan dinki da janaretocin wutar lantarki da injunan nika da firiji-firiji da kuma Naira miliyan 15, shugaban marasa rinjaye a Majilisar Wakilai Cif Femi Gbajabiamila na Jam’iyyar APC ya raba wa jama’ar mazabarsa ta Surulere a Jihar Legas.Haka kuma ya gina rijiyoyin burtsatse biyu ga barikin Abalti da ke unguwar […]
Kayayyakin da suka hada da kekunan dinki da janaretocin wutar lantarki da injunan nika da firiji-firiji da kuma Naira miliyan 15, shugaban marasa rinjaye a Majilisar Wakilai Cif Femi Gbajabiamila na Jam’iyyar APC ya raba wa jama’ar mazabarsa ta Surulere a Jihar Legas.
Haka kuma ya gina rijiyoyin burtsatse biyu ga barikin Abalti da ke unguwar Ojuelegba don rage matsalar ruwan da jama’a ke fuskanta wadanda aka kaddamar a lokacin raba kayayyakin a harabar barikin.
Da yake jawabi jim kadan da mika wa wadanda sunayensu suka samu cin wannan gajiyar, dan majilisar ya ce wannan ba shi ne karshe ba, domin abin sai ana yi ana agaza wa jama’a saboda halin kunci da damuwa da yawancin ’yan Najeriya ke fuskanta, lamarin da ya zamo hasali ma talaka bai jin kowane yare idan ba na yaya za a taimaka masa ba.
Cif Gbajabiamila ya ce duk da yake ba aikin dan majalisa ba ne samar da ababen more rayuwa ko tallafi irin wadanda ya raba, amma yanayin da kasar ta samu kanta ne ya sa dole sai ana yi ana taimaka wa masu karamin karfi. Ya ba da hakuri ga wadanda ba su tallafin ba cewa su jira gaba.
Wannan tallafi bai takaita ga ’yan asalin Jihar Legas kawai ba, har mutanen Arewa mazauna can sun amfana, ciki har da wadanda ba ’yan jam’iyyarsu ta APC ba.
Yayin da wakilinmu ya tambaye shi bai ganin za a ce domin ya ga zabe na karatawo ne ya sa ya ba da tallafin ba, sai Cif Femi ya ce, “Duk wanda ya ce dabara ce ta kamfe, to shi ma ya je ya yi hakan. Ai kowa na da tasa irin dabarar. Alhali ma ba gaskiya ba ne domin jama’ar da nake wakilta sun san cewa wannan ba shi ne karo na farko da na rarraba kayayyaki ba.”
Wasu daga cikin ’yan Arewa da suka ci wannan gajiyar, irin su Alhaji Idris Musa Birniwa da aka ba firiji, ya ce ba abin da za su ce sai Allah Ya saka masa da alheri, domin duk lokacin da ya tashi ba da irin wannan tallafin, bai mance ’yan Arewa, kuma wannan yana kara musu kwarin gwiwar cewa ba a kallon su a matsayin baki a jihar.