dan Maraya: Malamin mawaka ya kwanta dama

En ehin duniya,  En ehin duniya, Duk wanda ya mutu ya huta, Mutuwa rigar wannan, Mutuwa rigar wancan, Mutuwa rigata ce,Da hali wallahi,Tawa ko da na tube, Ka tabbata da na kyautar. – Adamu dan Maraya Jos a wakarsa ta Mutuwa Rigar Kowa. Allahu Akbar, mutuwa ta cimma wannan bawan Allah a ranar Asabar da […]

dan Maraya: Malamin mawaka ya kwanta dama
dan Maraya: Malamin mawaka ya kwanta dama

En ehin duniya, 

En ehin duniya,
Duk wanda ya mutu ya huta,
Mutuwa rigar wannan,
Mutuwa rigar wancan,
Mutuwa rigata ce,
Da hali wallahi,
Tawa ko da na tube,
Ka tabbata da na kyautar.
– Adamu dan Maraya Jos a wakarsa ta Mutuwa Rigar Kowa.

Allahu Akbar, mutuwa ta cimma wannan bawan Allah a ranar Asabar da ta gabata kuma wakilinmu ya rubuto mana ta’aziyyarsa kamar haka:
A ranar Asabar da ta gabata ne Allah Ya yi wa wannan shaharraren mawaki mai kidan kuntigi, Alhaji Adamu dan Maraya Jos rasuwa bayan ya yi fama da ciwon da aka yi hasashen sankarar baki ne.
Mawakin ya rasu a wani asibitin kudi mai suna Martami Hospital da ke Jos bayan Sallar Azahar din ranar.
Alhaji Yusuf Kucilla babban dan da marigayin ya rike, kasancewar Allah bai ba shi haihuwa ba ya bayyana yadda marigayin ya yi jinya har zuwa ajalinsa.
Kucilla ya ce: “Dokta, baba ne a wurinmu, ya kwanta rashin lafiyar nan ba da dadewa ba, tun ranar da aka yi zaben Shugaban kasa bai sake fitowa ba, idan ya fito sai idan za a kai shi asibiti, abin da yake daga min hankalin dangane da rasuwarsa shi ne, dimbin yaran da ke karkashinsa da yake kula da su.”
Ya ce marigayin ya rasu a asibitin kudi da ake kira Martami, amma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) yake zuwa a duba lafiyarsa, “Kasancewar likitocin JUTH suna yajin aiki, sai suka ba mu shawarar mu kai shi Asibitin Martami duk abin da za su iya, to a Martami ma za a iya yi masa, a ranar da za mu kai shi can asibitin mun je mun samu likitoci hudu suna jiran zuwanmu.”
Ya tabbatar da marigayi dan Maraya bai taba haihuwa ba, sai dai ya rike dimbin yara, inda ya dauki nauyin karatunsu, ya kuma aurar da mata da yawa.
Alhaji Sa’idu Sasuwai makadin Shata wanda mahaifiyarsa ta yi wa marigayin uwar daki, ya bayyana cewa duk abin da wa yake yi wa kane, to, marigayi ya yi musu, abin da ya fi daukar hankalinsa dangane da marigayin shi ne, yadda ya karbi wata yarinya ’yar kabilar Jarawa da ake kira Maryam a wurin mahaifinta ya Musuluntar da ita har ya aurar da ita.
“Ya dauke mu kannensa tunda a dakin gyaturmamu ya tashi, ba shi da mugunta, yana da kyauta, komai ya samu zai ba mu, ya ba mu sutura da abinci da kudi, sannan idan yana gida tare muke cin abinci da shi,” inji Sasuwai.
Ya ce dan Maraya ya ba duniya gudunmuwa ta hanyar wakoki, “Domin wakokinsa babu ashararanci, yana waka kamar yana tafsiri, ba ya yin waka sai ya tabbatar da cewa za ta amfani jama’a ko gwamnati.”
Alhaji Sasuwai ya ce hirar da ya yi da marigayin ta karshe ita ce, bayan ya zo gidan marigayin sai ya ce masa ba shi da lafiya, to a lokacin zai tafi Abuja saboda limamin masallacin Abuja wanda amininsa ne ya rasu. “A nan muka yi sallama, sai dai kafin in dawo ciwon ya yi tsanani,” inji shi.
Anas dan Maraya wanda yake tare da marigayin a asibiti har ya rasu, wanda kuma marigayin yake sirri da shi ya bayyana cewa dan Maraya ya hore su da su kasance masu bin doka da oda.
“Jama’a suna magana a kansa cewa mutumin kirki ne, kuma tunda nake tare da shi ban taba jin ko ganin wani a matsayin abokin hamayyarsa ba, shekara goma sha da ni yake komai, duk abin da zai yi, to, ni ne a gaba, duk abin da zai yi da ni yake shawara. Ya ba mu tarbiyya, ya dora mu a kan tafarkin bin addini sau da kafa, ya umarce mu mu kasance masu bin doka da oda, mu guji cin hanci da rashawa,” inji shi.
Anas ya ce marigayin ya yi masa wasiyyar ya zauna da mutane lafiya.
Maidakin marigayin Hajiya Hafsatu wanda aka fi sani da Hajiya Sabuwa, ta ce ba su taba samun sabani a tsakaninsu ba, dukkansu suna gudun bata wa juna rai, ta kuma yi masa duk wata biyayya da ta kamata mata ta yi wa mijinta.