Dan Masar ya lashe gasar kirkira ta Afirka

An gudanar da taron bayar da lambar yabo ta kirkire-kirkire na nahiyar Afirka na wannan shekarar a birnin Accra na kasar Ghana. BBC ta ruwaito cewa matasa goma ne aka zabo daga kasashen nahiyar Afirrka don shiga wannan gasar ta kere-kere, cikinsu har da Najeriya. Taron na bana shi ne karo na shida da ake […]

Dan Masar ya lashe gasar kirkira ta Afirka

An gudanar da taron bayar da lambar yabo ta kirkire-kirkire na nahiyar Afirka na wannan shekarar a birnin Accra na kasar Ghana.

BBC ta ruwaito cewa matasa goma ne aka zabo daga kasashen nahiyar Afirrka don shiga wannan gasar ta kere-kere, cikinsu har da Najeriya.

Taron na bana shi ne karo na shida da ake yi da nufin zaburar da matasa da basu kwarin gwiwar kirkiro abubuwan da al’umma za su amfana da shi.

Dakta Olawale Olanisolu dan Najeriya ne, kuma likitan kirji, wanda kuma shi ne ya kirkiro wata na’urar gwaji don gano cutar tarin fuka cikin minti 10, ba a bukatar daukar jini ko fitsari yayin wannan gwajin, gumin jikin dan Adam ake bukata wajen wannan gwajin.

Sai dai kuma wani dan kasar Masar ne mai shekara 58 farfesa Aly El Shafei wanda malami ne a jami’ar birnin Alkahira ne ya yi nasarar lashe gasar ta bana.

Ya yi nasarar lashe kyautar dala 100,000 yayin da wanda ya yi na biyu kuma zai dauki dala 25,000, sannan kuma akwai lambar yabo ta musamman ga wanda ya kirkiro abinda ya yi tasiri sosai a kan al`umma. 

Shi ma za a bashi dala 25,000, sannan kuma sauran mutane bakwai da ke cikin gasar, ko wanne zai samu dala dubu biyar-biyar, sannan kuma daga baya, akwai wani shirin samar musu tallafin ci gaba da ayyukansu.