Dan Najeriya na iya zama a ko’ina – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya nemi mutanen Arewa da su yi hakuri da ‘yan uwansu na kudancin Nijeriya su ko su girmama al’adun mutanen Arewa a zauna lafiya, ko’ina mutum yana iya zama ba sai inda aka haife shi ba.  Sarkin Musulmi ya yi wadannan kalamai ne a jawabinsa na Barka da Sallah ga […]

Dan Najeriya na iya zama a ko’ina – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya nemi mutanen Arewa da su yi hakuri da ‘yan uwansu na kudancin Nijeriya su ko su girmama al’adun mutanen Arewa a zauna lafiya, ko’ina mutum yana iya zama ba sai inda aka haife shi ba. 

Sarkin Musulmi ya yi wadannan kalamai ne a jawabinsa na Barka da Sallah ga al’ummar musulmin kasar nan, inda ya ce “Ba wani mutum da ya isa ya kori kowa, mu san muhimmancin zama da wanda ba musulmai ba, a zauna lafiya kamar yadda Allah Ya hadamu duk wanda ke wurinka ka tallafa masa iya kokarinka, a guji kalaman batanci, addininmu shi ne rayuwarmu rayuwarmu, ita ce addininmu kowa ya zauna in da yake cikin girmamawa da mutuntawa,” a cewar Sarkin Musulmi. 

Ya kara da fadin cewa, a jagoranci duk inda aka samu shugaba na kwarai za a samu mabiya na kwarai, in ka ga mabiya marasa kirki to a bincika yana yiwuwa shugaban tare da su yake. Sannan sai ya yabawa gwamnatin Buhari da ta baiwa sha’anin tsaro da noma muhimmanci.