Dan Najeriya ya bindige mahaifiyarsa a Amurka
Wani yaro mai shekara 12 dan asalin Najeriya ya bindige mahaifiyarsa har lahira a Amurka bisa kuskure.
Wani yaro mai shekara 12 dan asalin Najeriya ya bindige mahaifiyarsa har lahira a Amurka bisa kuskure.
Kafar yada labarai ta CBS ta ruwaito cewa, wannan al’amari ya auku ne ranar Litinin a gidan su yaron da ke Forestdale, Alabam a Amurka, inda ajalin gyatumar mai suna Ayobiyi Abeni Harris Cook, ya cim mata.
- Jirgin yaki ya kashe kasurgumin dan bindiga Alhaji Shanono da yaransa 18
- Real Madrid ta lashe kofin UEFA Super Cup na 5
Bayanai daga yankin sun nuna cewa, lokacin da abin ya faru, mahaifin yaron, Djuan Cook wanda dan sanda ne, yana wurin aiki.
Rahoton hukuma ya nuna da farko yaron ya yi wa jami’an bincike karya kan dalilin mutuwar mahaifiyar tasa.
Ya fada wa hukuma wai barawo ne ya shigo gidan ya harbe ta sannan ya gudu.
Amma da aka matsa da bincike, daga bisani yaron ya yi ikirarin shi ne ya kashe ta.
Hukumomi sun ce bayan kammala bincike za a gabatar da batun a kotu.
Djuan Cook, ya ce za a yi jana’izar matar tasa ya zuwa ranar 12 ga Agusta inda za a hadu a yi ban-kwanan karshe da ita.